Babu tantama a kan mutunci da kimar Buhari - Obasanjo karami

Babu tantama a kan mutunci da kimar Buhari - Obasanjo karami

Jagoran kungiyar Buhari Youth Organisation (BYO), Olujanwo Obasanjo ya ce babu wani da ke tantama kan kima da mutuncin shugaba Muhammadu Buhari a matsayinsa na shugaba.

Dan tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjon ya ce shugaba Buhari ya fita daban cikin sauran shugabanin da suka mulki Najeriya saboda yadda ya ke tafiyar da dukiyar kasar.

Sai dai ya ki kwatanta gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da na mahaifinsa inda ya ce yanayin da suka tsinci kansu ba daya ya ke ba.

Babu tantama a kan mutunci da kimar Buhari - Obasanjo karami

Babu tantama a kan mutunci da kimar Buhari - Obasanjo karami
Source: Facebook

Obasanjo karamin ya yi wannan jawabin ne a yayin da ya ke hira da manema labarai a kan dalilin da yasa ya ke ganin ya dace 'yan Najeriya su sake zaben Buhari karo na biyu inda ya kara da cewa matasa ne su kafi amfana da shirye-shiryen da wannan gwamnatin ta bullo da su.

DUBA WANNAN: 'Yan majalisar dokokin jihar APC sun tafi yajin aiki saboda rashin biyansu alawus

Ya ce, "Buhari mutum ne mai son tallafawa matasa hakan ne yasa aka kafa kungiyar BYO. Wannan gwamnatin ta bawa matasa tallafi domin fara noma da kasuwanci.

"Wannan gwamnatin tana dora kasar a kan turban cigaba a fannin tattalin arziki da ayyukan more rayuwa."

Olujanwo ya ce goyon bayan Buhari da ya keyi bai shafi dangantakar da ke tsakaninsa da mahaifinsa ba.

"Ni shiga wannan tafiya ne saboda nayi imani da irin ayyukan da gwamnatin nan ke yi. Siyasa ba zai raba ni da mahaifi na ba. Muna kaunar juna kamar yadda kowane iyali suke son junansu.

"Ya kamata siyasa ta hadan kan al'umma ne ba raba su ba. Yana da muhimmanci mu ajiye banbancin addini, kabilar ko bangaranci a gefe guda," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel