Hukumar Sojin Ruwa ta cafke 'yan Kasar Kamaru 6 da Sumoga ta Shinkafa a jihar Cross River

Hukumar Sojin Ruwa ta cafke 'yan Kasar Kamaru 6 da Sumoga ta Shinkafa a jihar Cross River

Dakarun sojin ruwa na Najeriya, sun samu nasarar cafke wasu 'yan kasar Kamaru 6 su na tsaka da aikata fasadi na fasakauri ta sumogar buhunan Shinkafa 700 daga kasashen ketare zuwa Najeriya shiyyar birnin Calabar na jihar Cross River.

Wannan miyagun mutane 'yan asalin kasar Kamaru da suka silalo cikin Najeriya ba tare da wani lasisi ba sun shiga hannu tare da wasu Mutane 7 'yan asalin kasar nan da ke aikata wannan mummunan fasadi mai barazanar zagon kasa ga ci gaban kowace kasa.

Jagoran cibiyar dakarun sojin, Kwamanda Julius Nwagu, ya mika wannan bakin haure zuwa ga hukumar shige da fice ta Najeriya yayin da ya danka hajarsu ta fasakauri ta kimanin Naira miliyan 11 zuwa ga hukumar Kastam ta kasa reshen Calabar.

Hukumar Sojin Ruwa ta cafke 'yan Kasar Kamaru 6 da Sumoga ta Shinkafa a jihar Cross River

Hukumar Sojin Ruwa ta cafke 'yan Kasar Kamaru 6 da Sumoga ta Shinkafa a jihar Cross River
Source: Depositphotos

A yayin da lokaci na shagulgulan bikin Kirsimeti ke ci gaba da karatowa, hukumar sojin ta bayyana cewa za ta kara kaimi wajen datse hanyoyinta domin cafke miyagun mutane musamman wajen aikata laifuka na fasakauri yayin neman tara da dukiya cikin gaggawa.

KARANTA KUMA: An yi garkuwa da 'Diyar Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Katsina

Mai kula da harkokin dakile fasakauri na hukumar Kastam, Akpan Ime Edet, ya bayyana cewa za su killace wannan tarin Shinkafa a dakunan ajiya na kayayyakin fasakauri yayin da sauran miyagun mutane bakwai 'yan asalin kasar nan za su fuskanci hukunci daidai da abinda suka aikata.

Cikin wani rahoto mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar ta Kastam ta samu nasarar cafke wasu kayayyakin fasakauri na kimanin Naira Miliyan 76 a reshenta na jihar Kano da Jigawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel