Babbar magana: 'Yan sanda sun kama AIG na bogi a arewacin Najeriya

Babbar magana: 'Yan sanda sun kama AIG na bogi a arewacin Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Sokoto ta sanar da cewar ta kama wani mutum mai suna Ibrahim Dangaladima da ke yin sojan gona a matsayin babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa (AIG).

DSP Cordelia Nwawe, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ne ta bayyana hakan a yau, Laraba, a garin Sokoto.

Nwawe ta kara da cewar Dangaladima ya dade a cikin jerin mutanen da hukumar 'yan sanda ke nema ruwa a jallo bisa laifukan damfara da sojin gona a cikin watanni hudu da su ka wuce.

"Karyar sa ta kare ne ranar Juma'a, 23 ga watan Nuwamba, bayan yin karyar cewar shine babban sifeton rundunar sanda tare da yin alkawarin samar da aiki ga aiki ga yaran wasu 'yan kasuwa.

Babbar magana: 'Yan sanda sun kama AIG na bogi a arewacin Najeriya

Shugaban rundunar 'yan sanda; Ibrahim Idris
Source: Depositphotos

"Ya nemi a bashi N482,500 ga duk takardar aiki ta ASP da N222,000 ga duk takardar aiki a matakin Inspekta."

"Bayan ya shiga hannu, ya tabbatar da cewar ya kai tsawon shekaru 5 yana aikata irin wannan damfara ga jama'a," a cewar Codelia.

DUBA WANNAN: Zan yi murabus idan APC ta lashe zaben jiha ta - Babban Sarki a arewa

Kazalika rundunar 'yan sandan ta yi bajakolin wani kwararren barawon mota mai suna Surajo Muhammad, dan asalin yankin Arkila a jihar.

A cewar kakakin, an kama Suraja a hannu yayin da yake tsaka da yunkurin sace mota a masallacin Shehu.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta dade tana neman Suraja kafin daga bisani ta samu nasarar kama shi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel