Tsohon dan takarar APC a Nasarawa ya koma ADC

Tsohon dan takarar APC a Nasarawa ya koma ADC

Mista Jacob Ajegana-Kudu, tsohon dan takarar kujerar majalisar dokoki akarkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Nasarawa, ya bar jam’iyyar ya koma jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Ajegana-Kudu ya rasa tikitin takara na dan majalisa mai wakiltan Nassarawa Eggon na gabas a majalisar dokokin jihar lokacin zaben fidda gwani.

Tsohon hadimin na Gwamna Tanko Al-Makura ya bayyana matsayarsa a wani taron manema labarai a Nassarawa Eggon a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba.

Tsohon dan takarar APC a Nasarawa ya koma ADC

Tsohon dan takarar APC a Nasarawa ya koma ADC
Source: Depositphotos

A cewarsa ya yanke shawarar komawa ADC ne sabda rashin adalci daa damkradiyya a APC.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya ziyarci dakarun sojojin da aka raunata

Ya kuma bayyana cewa kwamitin da APC ta nada domin yin sulhu ga fusatattun mambobinta sun gaza magance matsalar bayan sun saurari kokensu.

Ya kuma godema shugabannin ADC na jihad a kasa baki daya inda yayi alkawarin cewa ba zai basu kunya a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel