Bayan bankuna sun shaqe bilyan 7 na daloli a 2010, yanzu Buhari yace dole su dawo dasu lalitar gwamnati

Bayan bankuna sun shaqe bilyan 7 na daloli a 2010, yanzu Buhari yace dole su dawo dasu lalitar gwamnati

- Fadar shugaban kasa tayi alkawarin yin duk abinda ya kamata don ganin ta dawo da dala biliyan 7 da babban bankin Najeriya ta bawa bankuna masu zaman kansu

- Gwamnatin tarayya tana binciken wani Dan siyasa

- Wani kamfanin mai da ya rike dala biliyan 1.6 na kudin shiga an binciko shi

Bayan bankuna sun shaqe bilyan 7 na daloli a 2010, yanzu Buhari yace dole su dawo dasu lalitar gwamnati

Bayan bankuna sun shaqe bilyan 7 na daloli a 2010, yanzu Buhari yace dole su dawo dasu lalitar gwamnati
Source: Depositphotos

Fadar shugaban kasa tayi alkawarin yin duk abinda ya dace don ganin babban bankin Najeriya ta dawo da dala biliyan 7 da ta bawa bankuna masu zaman kansu a 2006.

Su dai bankunan sunce kyauta ce gwamnati tayi musu da kudin jama'a, lamari da shugaba Buhari yace sam-sam ba zai iyu ba, qara wa mai karfi karfi. Dole a dawo da kudin Dala biliyan shidda domin talakawa su mora.

Shugaban kwamitin Fadar shugaban kasa akan dawo da kudin kasa, Mista Okoi Obla-Obono, ya tabbatar da hakan a wani taro da kungiyar ma'aikatan gwamnati ta shirya akan cece kucen OPL 245 a Abuja.

DUBA WANNAN: Duniya na Allah-wadai da Saudiyya saboda ta dawo taimakawa zafin ra'ayin Islama

Obla-Obono yace Gwamnatin tarayya tana binciken wani dan siyasa akan kamfanonin shi 20 a turai don gujewa biyan haraji ga Najeriya.

Shugaban Kwamitin, ya kuma bayyana wata masana'antar mai da ta rike dala biliyan 1.9 na kudin shigar Najeriya don haka za'a hukunta masana'antar da laifin yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel