Buhari: Zan dawo da likitocinmu da suka tsere kasashen masu kudi gida Najeriya

Buhari: Zan dawo da likitocinmu da suka tsere kasashen masu kudi gida Najeriya

- Zamu dawo da kwararru kan harkar lafiya dake kasashen ketare zuwa gida Najeriya

- Aduk shekara suna Samar da kudi sama da 20m

- Gwamnatin zata bada goyan baya akan duk wani kasuwanci da za'a kawo kasar

Buhari: Zan dawo da likitocinmu da suka tsere kasashen masu kudi gida Najeriya

Buhari: Zan dawo da likitocinmu da suka tsere kasashen masu kudi gida Najeriya
Source: Twitter

Shugaban kasa Muhammad Buhari yace za'a dawo da kwararru kan harkar lafiya dake kasashen ketare zuwa gida Najeriya don su tallafa.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake karbar wani tayin kasuwanci a fadar sa dake Abuja.

Mataimakin Shugaban kasa na musamman akan harkar kasuwanci da kasashen ketare tare da hadin gwiwar NIDAN ne suka hada wannan taro.

Mataimakin Shugaban kasa Prof Yemi Osinbajo da yake wakiltar Shugaban yace gwamnatin tarayya a shirye take da ta bawa dukkanin wata harkar kasuwan goyan baya matukar za'a samu abinda ake nema.

DUBA WANNAN: Duniya na Allah-wadai da Saudiyya saboda ta dawo taimakawa zafin ra'ayin Islama

Yace a kowace shekara yan Najeriya dake wasu kasashen suna turowa da kasar kudi sama da dala biliyan 20.

Ya kara da cewa kasar zata samar da wani waje wanda zai bata damar aiwatar da irin wannan kasuwanci a cikin kasar don ta amfana.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel