An yankewa magini hukuncin daurin shekaru 5 saboda yiwa karuwa fyade

An yankewa magini hukuncin daurin shekaru 5 saboda yiwa karuwa fyade

A yau, Laraba, ne wata kotun jihar Legas ta musamman da ke sauraron karar rikicin ma'aurata da cin zarafin mata ta yankewa wani magini, Edet Imoh, hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari saboda aikata fyade ga wata karuwa.

Alkaliyar kotun, Uwargida Sybil Nwaka, ta hana Imoh zabin biyan tarar kudi tare da bayyana cewar hakan zai zama darasi ga ma su sha'awar aikata irin laifin Imoh.

"Na samu wanda ake zargi da aikata laifin cin zarafi, na yanke ma sa hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari da zai fara daga yau.

"Ina fatan lokacin da za ka fito daga yari ka gane kuskuren ka kuma ka yiwa kan ka fada," a kalaman alkaliyar kotun.

An yankewa magini hukuncin daurin shekaru 5 saboda yiwa karuwa fyade

An yankewa magini hukuncin daurin shekaru 5 saboda yiwa karuwa fyade
Source: Twitter

Uwargida Nwaka ta yiwa karuwar, Ejiro Umukoro, hudubar cewar ta guji sana'ar karuwanci domin haramtacciyar sana'a ce da yanzu haka gwamnatin jihar Legas ke kokarin yin sabbin dokoki a kanta.

"Na ja kunnen mai karar da ta zama mai hali nagari.

"Ina son yin amfani da wannan dama na sanar da duk masu sana'ar karuwanci da su sake tunani domin neman sana'ar ta kirki tun kafin gwamnatin jihar Legas ta kaddamar da shirin da ta ke yi na yaki da sana'ar karuwanci.

DUBA WANNAN: Zan yi murabus idan APC ta lashe zaben jiha ta - Babban Sarki a arewa

"Gwamnatin jihar Legas na matukar jin ciwon wannan sana'ar ta karuwanci kuma tana shirin daukan mataki a kan ma su yinta," a kalaman uwargida Nwaka.

Sai dai wanda ake karar ya ce bai aikata laifin da ake tuhumar sa da shi ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar lauya mai gabatar da kara ya shaidawa kotu cewar wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2017 a unguwar Ikoyi dake garin Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel