Gwamnati zata samar muku makamai domin ku kawar da Boko Haram daga doron kasa - Buhari

Gwamnati zata samar muku makamai domin ku kawar da Boko Haram daga doron kasa - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a matsayinsa na shugaban kasa da kuma karfin da yake da shi, zai tabbatar da cewa gwamnati ta samar da makaman yakin zamani domin kawar da haukan Boko Haram.

Buhari ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi a birnin Maiduguri, jihar Borno a yau Laraba, 28 ga watan Nuwamba yayinda ya tafi halartan taron babban hafsan sojin Najeriya da ke gudana a jihar.

Ya jajintawa hukumar sojin Najeriya bisa ga rashin akalla sojoji 44 da sukayi a makon da ya gabata sakamakon harin Boko Haram kan barikin Matele dake arewacin jihar Borno.

Buhari yace: “A matsayina na shugaban kasa da kuma karfin da aka bani, ina tabbatar muku da cewa gwamnatin zata sama muku makaman zamani domin kawar haukan Boko Haram da kuma wasu ayyukan makiyanmu.”

“Kana ina kara tabbatar muku da cewa gwamnati na iyakan kokarinta wajen kara alatun jin dadin jami’an sojinmu.”

A cikin jawabinsa, Shugaba Buhari ya bayyana cewa akwai wadansu masu yiwa jami’an soji isgili idan Iftila’I ya same su.

Ya yi kira da kada hakan ya rage musu karfin guiwa ko ya dauke musu hankali wajen gudanar da aikinsu.

Mun kawo muku cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa Maiduguri, babbar birnin jihar Borno don kaddamar da bude taron ma'aikatan hukumar soji na shekara-shekara da ke gudana a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel