Mun san wadanda basu taba yabawa aikunku ba zasu muku dariya idan kuka samu rashi – Buhari ga Sojoji

Mun san wadanda basu taba yabawa aikunku ba zasu muku dariya idan kuka samu rashi – Buhari ga Sojoji

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da dogon jawabi a birnin Maiduguri, jihar Borno a yau Laraba, 28 ga watan Nuwamba yayinda ya tafi halartan taron babban hafsan sojin Najeriya da ke gudana a jihar.

Buhari ya yi Allah wadai da yadda wasu yan siyasa ke amfani da rashin da sojojin sukayi sakamakon harin da yan Boko Haram suka kai kwanakin nan inda ya zaburar da Sojin da su cigaba da jajircewa duk da makircin makirai.

Buhari yace: “Tuni muna sane cewa wadanda basu taba yabawa namijin kokari da nasarorin da kuke samu ba, sune masu muku isgili idan suka samu cibaya”

“Kada ku damu da abubuwan da makirai ke fadi. Ku cigaba da jajircewa kuma ku kawar da Boko Haram a doron kasa.”

Za ku tuna cewa uwar jam'iyyar APC ta yi kaca-kaca da PDP kan yadda sukayi isgili da mutuwan akalla sojojin Najeriya 44 a harin da yan Boko Haram suka kai barikin sojojin da ke Matele a makon da ya gabata.

KU KARANTA: Uwargida ta yiwa amarya wanka da manja a wajen biki (Hotuna)

Mun kawo muku cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa Maiduguri, babbar birnin jihar Borno don kaddamar da bude taron ma'aikatan hukumar soji na shekara-shekara da ke gudana a jihar.

An mayar da taron jihar Borno daga jihar Edo ne sakamakon rashin da hukumar tayi a garin Matele.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel