'Yan majalisar dokokin jihar APC sun tafi yajin aiki saboda rashin biyansu alawus

'Yan majalisar dokokin jihar APC sun tafi yajin aiki saboda rashin biyansu alawus

Mambobin majalisar jihar Kogi sun tafi yajin aiki saboda nuna bacin ransu ga rashin biyansu kudaden allawus din yiwa mazabunsu ayyuka da gwamnatin jihar ba tayi ba na sama da shekara guda.

Daily Trust ta ruwaito 'yan majalisar sun dawo daga hutun makonni biyu da suka tafi a ranar Talata amma ba suka sake tafiya yajin aiki saboda rashin biyan kudaden.

'Yan majalisar sun hallara zuwa harabar majalisar misalin karfe 10 na safiya inda su kayi wani taro na shugabani da suka saba yi kafin fara zaman majalisar.

'Yan majalisar dokokin jihar APC sun tafi yajin aiki saboda rashin biyansu alawus

'Yan majalisar dokokin jihar APC sun tafi yajin aiki saboda rashin biyansu alawus
Source: Depositphotos

Sai dai bayan kammala taron, zaman majalisar bai yiwu ba saboda galibin 'yan majalisar sun tattara sun fice daga zauren majalisar saboda rashin biyan allawus din.

DUBA WANNAN: Badakalar N29bn: Yadda wasu shaidu a tuhumar Nyako su ka yi mutuwar ban mamaki

An gano cewa kakakin majalisar, Mathew Kolawole da wasu tsirarun 'yan majalisar da su kayi saura a zauren majalisar sun kasa gudanar da wani aiki saboda adadinsu ya yi kadan.

Wani dan majalisa da ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce 'yan majalisan sun fusatta ne saboda gwamnatin ta biya 75% na cikin allawus dinsu na 2017 kuma har yanzu ba a biya su ko sisi ba cikin allawus din 2018.

Ya ce fusatattun 'yan majalisar sun rantse cewa ba za su cigaba da zamansu a majalisar ba har sai gwamnatin jihar ta biya su hokokinsu saboda da wannan kudin ne suke yiwa al'ummar mazabunsu ayyukan more rayuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel