Daga karshe: Rundunar 'yan sanda ta kori jami'inta da ya kashe wani dalibin jami'a

Daga karshe: Rundunar 'yan sanda ta kori jami'inta da ya kashe wani dalibin jami'a

- Rundunar 'yan sanda a jihar Bayelsa ta ce ta sallami wani jami'inta mai mukamin Sajen daga aiki, wanda ya harbe wani dalibin jami'a a ranar 23 ga watan Nuwamba

- Ainim Butswat, mai magana da yawun rundunar, ya kara da cewa nan ba jimawa ba za'a gurfanar da jami'in gaban kotu

- A wani labarin, al'ummar da ke zaune a unguwar Tenacious, yankin Edipie da ke Yenagoa, na ci gaba da bayyana korafinsu kan yadda rundunar 'yan sanda ke cin zarafinsu

Rundunar 'yan sanda a jihar Bayelsa ta ce ta sallami wani jami'inta mai mukamin Sajen daga aiki, wanda ya harbe wani dalibin jami'a mai shekaru 20 har lahira, mai suna Tariela Nikadae, a ranar 23 ga watan Nuwambar wannan shekarar.

Ainim Butswat, mai magana da yawun rundunar, wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Laraba a garin Yenagoa, ya kara da cewa nan ba jimawa ba za'a gurfanar da jami'in gaban kotu.

Lamarin dai ya faru ne a lokacin wani sumame da tsare wasu mazauna wata unguwa da sashen rundunar na SARS ya gudanar.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Na kashe budurwata saboda tana soyayya da yayana - Dan shekaru 16

Daga karshe: Rundunar 'yan sanda ta kori jami'inta da ya kashe wani dalibin jami'a

Daga karshe: Rundunar 'yan sanda ta kori jami'inta da ya kashe wani dalibin jami'a
Source: Facebook

Daga baya rundunar 'yan sandan ta tantance wadanda take tsare da su bayan da 'yan uwansu suka sanya baki.

"Rundunar 'yan sanda ta yi matukar bakin cikin lamarin da ya faru tsakanin jami'inta da jama'ar da ke zaune a unguwar Tenacious, Edipie a Yenagoa.

"Sajen Timadi Emmanuel wanda ke aiki a sashen rundunar na Akenfa, a wani sumame da suka kai a unguwar Tenacious, yankin Edepie, ba tare da wani dalili ba, ya harbe Tariela Nikade, mai shekaru 20

"Rundunr 'yan sanda ta kori jami'in bayan gudanar da bincike kan yadda lamarin ya faru, kuma nan bada jimawa ba za a gurfanar da shi gaban kotu da zaran mun kammala bincike," acewar Butswat.

A wani labarin, al'ummar da ke zaune a unguwar Tenacious, yankin Edipie da ke Yenagoa,na ci gaba da bayyana korafinsu kan yadda rundunar 'yan sanda ke cin zarafinsu.

Da yawa daga cikinsu sun shaidawa NAN cewa jami'an rundunar 'yan sandan basu tantance su ko sauraron korafe korafen su ba, haka kawai suka kama su suka rufe su.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel