ICPC ta gurfanar da tsohon babban sufetan Yansandan Najeriya gaban kotu kan satar N16, 400, 000

ICPC ta gurfanar da tsohon babban sufetan Yansandan Najeriya gaban kotu kan satar N16, 400, 000

Hukumar yaki da rashawa da makamantan laifukan, ICPC, ta gurfanar da tsohon babban sufetan Yansandan Najeriya a zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Sunday Ehindero tare da wani tsohon kwamishina John Obaniyi gaban kotu akan zarginsa da satan kudi.

Legit.com ta ruwaito ICPC na zargin Sunday da John ne da wawuran makudan kudade da suka kai naira miliyan goma sha shida da dubu dari hudu (N16, 400, 000) inda suke tuhumarsu da aikata laifuka goma a gaban babbar kotun babban birnin tarayya Abuja dake Apo.

KU KARANTA: Wani dan tatsitsin yaro mai shekaru 16 ya halaka budurwarsa saboda tana neman Yayansa

ICPC ta gurfanar da tsohon babban sufetan Yansandan Najeriya gaban kotu kan satar N16, 400, 000

Sunday
Source: Twitter

Lauya mai shigar da kara, O.G Iwuagwu ya bayyana ma kotun cewa tsohon babban sufetan Yansanda Sunday Ehindero da tsohon kwamishinan Yansanda John sun tafka wannan laifi ne a tsakanin watan Mayu na shekarar 2006 zuwa Nuwamban 2006.

A cewar Lauyan, manyan hafsoshin Yansandan biyu sun antaya wasu makudan kudade ne da suka kai naira miliyan dari biyar cikin wasu asusun banki na musamman guda biyu, ya kara da cewa gwamnatin jahar Bayelsa ce ta baiwa rundunar Yansandan Najeriya N557,995,065 don ta sayi makamai.

Lauya O.G ya cigaba da fede biri har wutsiya inda yace bayan wani dan lokaci da zuba kudaden nan cikin asusun bankin, sai suka samar da riban naira miliyan goma sha shida da dubu dari hudu da dari uku da goma sha biyar da kwabo shida (N16, 412, 315.06)

Kuma hakan laifi ne a karkashin doka kamar yadda lauyan ya bayyana ma kotu, inda yace laifin ya saba ma sashi na 26 (1) da sashi na 22 (5) na kundin dokokin yaki da rashawa na ICPC na shekarar 2000.

Sai dai wadanda ke tuhuma, tsohon babban sufetan Yansandan Najeriya Sunday Ehindero da tsohon kwamishinan Yansanda John Onibiyi sun musanta duk tuhume tuhumen da ICPC ke musu, inda lauyansu ya nemi kotu ta bada belinsu.

Daga karshe Alkalin kotun, mai sharia Sylvanus Orji ya bada belin wadanda ake kara, sa’annan ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Janairu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel