Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da zabin Buhari a matsayin sakataren EFCC

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da zabin Buhari a matsayin sakataren EFCC

Majalisar dattawa a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba ta taatar da nadin Olanipekun Olukoyede a matsayin sakataren hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) kasa da sa’o’i 24 bayan an dakatar da hakan.

An dakatar da tabbatar dashi a ranar Talata, 27 ga watan Nuwambba bayan wani mamba a kwamitin majalisa kan yaki da rashawa, Isa Misau ya zargi kwamitin da shirya wani rahoto ba tare da sanin sauran mambobinta ba.

Misau ya yi korafin cewa rahoton na dauke da sa hannun mutane uku kawai ne cikin mambobi takwas na kwamitin.

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da zabin Buhari a matsayin sakataren EFCC

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da zabin Buhari a matsayin sakataren EFCC
Source: Depositphotos

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a wata wasika mai kwanan wata 10 ga watan Satumba, 2018 ya zabi Olanipekun Olukoye, shugaban ma’aikata na shugaban EFCC, Ibrahim Magu a matsayin sakataren hukumar.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta yi karin haske game da yanayin ziyarar da Buhari ya fasa kaiwa Daura

A baya mun ji cewa Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan yaki da rashawa, Sanata Chukwuka Utazi ya yaba ma kokarin hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) a kan yaki da suke yi da rashawa.

Ya kuma bukaci mukaddashin shugaban hukumar, Ibrahim Magu da ya rubanya kokarinsa don ceto Najeriya daga matsalar rashawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel