Wani dan tatsitsin yaro mai shekaru 16 ya halaka budurwarsa saboda tana neman Yayansa

Wani dan tatsitsin yaro mai shekaru 16 ya halaka budurwarsa saboda tana neman Yayansa

Wani dan tatsitsin yaro dan shekara 16 mai suna Muhammadu ya halaka wata yarinya mai suna Fatima Isah a kauyensu dake Evutagi cikin karamar hukumar Katcha na jahar Neja saboda wai bata sonsa, ba ta yarda ta aureshi ba.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Muhammadu ya bayyana cewa kishi ne ya kwasheshi har ta kai ga ya halaka Fatima bayan taki amincewa da shi, inda ta nuna karara tafi son yayansa, don haka ita kam ba tsararsa bace.

KU KARANTA: Tafiyan Buhari: Osinbajo ya wakilci Buhari a wani muhimmin tattaunawa

Bugu da kari maganan aure tsakanin Fatima Isah da yayan Muhammadu ya kankama, tun bayan da mahainta Isah Evutagi ya bayyana amincewarsa ga yayan Muhammadu daya auri diyarsa Fatima.

Amma rahotanni sun ruwaito cewa Muhammadu ya dade yana barazanar kashe Fatima idan har bata yarda ta aureshi ba, kaji rigima irin na dan tatsitsi da bai tafasa amma ba har ya kone, wannan barazana yasa mahaifinta Isah ya kai kararsa zuwa wajen Yansanda, kimanin shekaru uku da suka wuce.

“Na sha fada ma yayana daya kyale min Fatima, saboda ina da burin aurenta, amma yaki sauraron duk maganan da nayi masa, kuma ya cigaba da zuwa wajenta, har zuwa ranar da raina y abaci na dauki adda na sassarata har sai da ta mutu.

“Kunga irin abinda hakan ya janyo min, yanzu na kashe mutum, duk da take a gidan yari zan gama rayuwata alhali inda dan shekara 16, gaskiya wannan ba abu bane mai kyau.” Inji shi.

Shima kaakakin Yansandan jahar Neja, Muhammad Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa, kuma dama a baya ya taba yin barazanar kasheta idan har bata daina ganin yayansa ba, ya kara da cewa zasu gurfanar dashi gaban kotu da zarar sun kammala bincike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel