Mutane 2 sun mutu bayan bada shaida kan Nyako

Mutane 2 sun mutu bayan bada shaida kan Nyako

Shaidu biyu da suka bada shaida mai muhimmanci kan tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, sunyi wani mutuwan ban mamaki.

Wani babban jami'an leken asirin hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, Adekunle Odofin, ya bayyanawa alkalin babban kotun tarayya dake zaune a Abuja yayinda aka zauna rana Talata.

Game da cewar NAN, Adekunle yace wadannan shaidun biyu sun bada shaidu masu muhimmanci kan binciken almundahanan N29 billion da ake zargin Murtala Nyako da shi.

Ana gurfanar da Gwamna Murtala Nyako tare da dansa, AbdulAziz Nyako, Abubakar Aliyu da Zulkiful Abba, kan laifuka 37 na yaudara, sata, cin dukiyan al'umma na biliyoyin nairori.

KU KARANTA: Hukumar EFCC tayi babban kamu, ta kwace manyan motoci 29

Ana tuhumar Nyako da amfani da kamfanoni biyar wajen karkatar da kudaden gwamnati. Kamfanonin sune Blue Opal Limited, Sebore Farms & Extension Limited, Pagoda Fortunes Limited, Tower Assets Management Limited and Crust Energy Limited.

Lauyan hukumar, Odofin, ya ce daya daga cikin shaidun wanda manaja ne bankin Zenith Bank mai suna Muhammad Iro, wanda ya bada shaida kumaya gabatar da takardun ya yi mutuwan fuji'a bayan bayar da hujja mai karfi ga kotu.

Kana diraktan wasu kamfanoni uku masu suna Ameak Investment Limited, Kirkelly Investment Limited da Pilkola Engineering Limited shi ma ya mutu bayan bada shaida.

Mutuwan wadannan mutane biyu ya baiwa kotun tsoro da kuma mamaki. Kana wannan abu zai iya baiwa wasu masu bada shaida tsoro gabatar da kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel