Ta tabbata asarar $6b Najeriya tayi, kuma wai harda Jonathan aka raba kudin na Malabu

Ta tabbata asarar $6b Najeriya tayi, kuma wai harda Jonathan aka raba kudin na Malabu

- Ana tsammanin gwamnatin Najeriya zata rasa dala biliyan 6

- Rashawar siyarda lasisin hakar mai na Shell da Oni

- Filin hakar man 245 yana daya daga cikin mafi girman filayen hakar mai a duniya

Ta tabbata asarar $6b Najeriya tayi, kuma wai harda Jonathan aka raba kudin na Malabu

Ta tabbata asarar $6b Najeriya tayi, kuma wai harda Jonathan aka raba kudin na Malabu
Source: Depositphotos

Gwamnatin Najeriya ta yi asarar dala biliyan 6 ($6b) saboda rashawa a gurin siyar da lasisin hakar mai na Shell da Oni a 2011.

Rijiyar hakar man tana daya daga cikin mafi girma a duniya wanda duk da zargin rashawa a kasar Italia da Najeriya.

A wani rahoton da Global Witness ta saki mai taken, 'Take the future: Shell' s scandalous deal for Nigeria's oil,' wanda tayi bincike akan harkokin cuwa-cuuwar a kasar nan.

"Cinikin lasisin OPL ya hada da rahoton da wanda aka bar Najeriya ba tare da kason ta na ribar ba daga wanda kason ta ne na rijiya man," inji rahoton.

DUBA WANNAN: Kada ka sake ka leko mana qasa, an gargadi Yariman Saudiyya kan taron G20

Rahoton yace cinikin ya take dokoki da yawa na kamfanin. Cinikin tsakanin Shell, Eni, jami'an gwamnatin Najeriya da kamfanin mai da iskar gas na Malabu ya bukaci sa hannun tsakanin Shell da Eni don raba aiyuka.

A binciken da aka yi a kasashen Turai, wanda aka fidda rahotonsa, an sanya sunan shugaba Jonathan a matsayin shine wani 'Fortunato" wanda ya karbi kudin cin hanci malala daga kudin.

Dama dai an tafka rashawa da cin hanci a zamanin PDP din wanda sai dai cewa sukayi kawaii a yafe musu, zasu tuba, a kuma zabe su a 2019.

Rahoton dai yace, kamfanin mai na shell da Eni da manyan shuwagabannin zamanin da aka yi cinikin, na fuskantar zargin cin hanci a kasashen Italia da Najeriya.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel