Kungiyoyin sa kai 5 sun gudanar da zanga-zangar kin jinin Buhari a ofishin jakadancin Amurka

Kungiyoyin sa kai 5 sun gudanar da zanga-zangar kin jinin Buhari a ofishin jakadancin Amurka

Wata gamayyar kungiyoyin sa kai wadanda ba na gwamnati ba da ake kira Coalition of Civil Society Organisations (CSOs) har su biyar sun gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a offishin jakadancin Amurka a garin Abuja.

Kungiyoyin dai sun bayyana cewa makasudin gudanar da zanga-zangar tasu shine domin nusasshe da kasar ta Amurka irin cin kashin gwamnatin ta shugaba Buhari ke yi wa demokradiyya musamman ma yayin da zabukan 2019 ke cigaba da karatowa.

Kungiyoyin sa kai 5 sun gudanar da zanga-zangar kin jinin Buhari a ofishin jakadancin Amurka

Kungiyoyin sa kai 5 sun gudanar da zanga-zangar kin jinin Buhari a ofishin jakadancin Amurka
Source: Facebook

KU KARANTA: An kama wani Fasto da matar aure

Legit.ng Hausa ta samu cewa shugaban gamayyar kungiyoyin, Mista Deji Adeyanju wanda yayi magana da manema labarai a madadin sauran kungiyoyin, yayi kira da kasar ta Amurka ta sa ido sosai wajen ganin hukumar INEC ta gudanar da sahihin zabe.

A wani labarin kuma, Wasu rahotannin da muke samu marasa dadin ji daga jihar Borno a Najeriya na cewa mayaka da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun sace mutane fiye da hamsin a yankin Gamborou kusa da iyaka da Kamaru.

Maharan dai kamar yadda muka samu sun kewaye mutanen ne a lokacin da suka je daji yin itacen hura wuta amma suka yi anfani da rashin tsaron dake a yankin suka yi awon gaba da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel