Dagwalon da ke PDP ba zai taba bari abin alheri ya gudana a jam'iyyar ba - Tsohon gwamnan jam'iyyar

Dagwalon da ke PDP ba zai taba bari abin alheri ya gudana a jam'iyyar ba - Tsohon gwamnan jam'iyyar

- Dan takarar shugabancin kasa na SDP, kuma tsohon gwamna Cross Rivers Donald Duke ya soki tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP

- Duke wanda ya fara neman tsayawa shugabancin kasa a PDP kafin komawa SDP ya ce matsalolin da ke jam'iyyar ba za su bari wani shugaba ya aikata alkhairi ba

- Ya ce idan an bashi tikitn takara a PDP kuma ya lashe zabe, matsalolin jam'iyyar ba zai barshi ya yi aiki yadda ya kamata ba

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Donald Duke ya ce matsalolin da ke tattare da jam'iyyar PDP ba zai bari shugaban kasa ya yi aiki ba ko da kuwa dan takarar jam'iyyar ne ya lashe zaben 2019.

Legit.ng ta gano cewa Duke ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis a Legas cewa duk irin kyakyawan niyyar da dan takarar ya ke dashi, dan takarar ba zai iya aiwatar da wasu ayyukan azo a gani ba muddin a karkashin jam'iyyar PDP ya lashe zabe.

PDP ba zata taba bari wani shugaban kasa ya tabuka abin arziki ba - Duke
PDP ba zata taba bari wani shugaban kasa ya tabuka abin arziki ba - Duke
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Magu ya nemi a dena kai shari'ar EFCC gaban wata alkaliya

Idan mai karatu bai manta ba, Duke yana cikin jerin masu neman tikitin takarar shugabancin kasa a PDP amma daga baya ya koma jam'iyyar SDP.

Ya ce: "Ko da ni na samu tikitin takarar shugabancin kasa a PDP kuma na lashe zaben 2015, matsalolin da ke tattare da jam'iyyar ba zai bari in tabbuka wani abin azo a gani ba.

"Rashawa ta yiwa jam'iyyar katutu. Dole sai mutum ya kasance yana da karfin zuciya da jajircewa kafin zai tsira daga rashawar da ta dabaibaye jam'iyyar," inji shi.

Duke ya kara da cewa wannan kalaman da ya fada ba wai domin adawa bane, ya fadi hakan ne saboda ya san gaskiya ne kasancewarsa tsohon wanda ya dade a jam'iyyar kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel