Gwamnatin jihar Ekiti ta kulle wasu manyan gine-gine na tsohon gwamna Fayose

Gwamnatin jihar Ekiti ta kulle wasu manyan gine-gine na tsohon gwamna Fayose

Gwamnatin jihar Ekiti, a karkashin shugabancin gwamnan jihar na yanzu Kayode Fayemi ta rufe wasu manyan gine-ginen da ake kyautata zaton na tsohon gwamnan jihar ne, Mista Ayodele Fayose a garin Ado Ekiti, babban birnin jihar.

Gine-ginen da gwamnatin ta rufe, ta bayyana cewa sun sabawa doka ne kuma ba su da lasisi daga gwamnatin ta jihar daga hukumar tsare-tsaren birane ta jihar watau Ministry of Housing, Physical Planning and Urban Development a turance.

Gwamnatin jihar Ekiti ta kulle wasu manyan gine-gine na tsohon gwamna Fayose

Gwamnatin jihar Ekiti ta kulle wasu manyan gine-gine na tsohon gwamna Fayose
Source: UGC

KU KARANTA: Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa ya koma APC a Bauchi

Legit.ng Hausa dai ta samu cewa gidajen da gwamnatin ta rufe suna a rukunin gidajen ma'aikatan gwamnatin jihar a kusa da gidan mataimakin gwamna duk dai a garin na Ado Ekiti.

A wani labarin kuma, Majalisar dattawan Najeriya a ranar Larabar da ta gabata mun samu cewa sun aike da takardar sammaci zuwa ga ministan shugaba Buhari na sufuri, Mista Rotimi Amaechi don jin bahasi game da hanyar jirgin kasan da ake yi daga Fatakwal zuwa Maiduguri.

Kwamitin sufuri ne dai na majalisar zai shirya karbar bakuncin ministan duk dai cewa har yanzu ba su saka ranar da zai bayyana a gaban na su ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel