Kyautan motoci 200 don tazarcen Buhari: Ba Ganduje bane ya bayar, kalli mutumin daya bayar

Kyautan motoci 200 don tazarcen Buhari: Ba Ganduje bane ya bayar, kalli mutumin daya bayar

An gano mutumin daya baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kyautan motoci dai dai har guda dari biyu don yakin neman sake zabensa karo na biyu a yayin zaben 2019, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Legit.com ta ruwaito da fari an fara yamadidin cewa gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya bada kyautan motocin ga Buhari saboda ya samu sauki a bahallatsar karbar cin hanci data dabaibaye shi, sai dai hadimin shugaba Buhari, Bashir Ahmad ya musanta haka.

KU KARANTA: Gwamnan Kano ya lashe kyautar gwarzon gwamnan nahiyar Afirka kwata

Yakubu G
Yakubu Gobir
Source: Twitter

Bashir ya bayyana gaskiyar wanda ya bada kyautan motocin ne a shafinsa na Twitter, inda yace duk masu watsa jita jitan wai Ganduje ne ya bada motocin karya suke yi, sa’annan yace Yakubu Gobir ne ya bada motocin.

Haka zalika shi kansa mai gayya mai aiki, Alhaji Yakubu Gobir ya tabbatar da maganan Bashir, inda yace tabbas shine ya bada motocin ba Ganduje ba, kuma ya bada motoci dari biyu ne don amfanin yakin neman zaben Buhari da Osinbajo a zaben 2019.

“Ni dan asalin jahar Kwara ne, kwararren ma’aikacin gwamnati ne, dan kasuwa ne, kwararren mai ilimin kimyyar hada magunguna ne, ina da iyali, ina da mata kuma cikakken dan siyasane ni.” Kamar yadda ya fadi a shafinsa na Twitter.

Kyautan motoci 200 don tazarcen Buhari: Ba Ganduje bane ya bayar, kalli mutumin daya bayar
Motoci
Source: UGC

Ga makarantun da Gobir ya yi karatu a rayuwarsa:

INSEAD GEMBA, Global Executive

MBA 2010 – 2011

Harvard Business School

OPM, Owner/ President Management Program

2008 – 2010

Ahmadu Bello University

B.PHARM, Pharmacy

1981 – 1985

Cheltenham College, UK

GCE 1976 – 1981

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel