Tallar turmi: Kamfanonin talla suna bijirewa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar

Tallar turmi: Kamfanonin talla suna bijirewa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar

Kamfanonin 'yan kasuwa dake tallata hajojin 'yan kasuwa da 'yan siyasa a Najeriya mun samu cewa suna cigaba da bijirewa karbar tallar dan takarar shugaban kasar Najeriya a 2019 na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, kamar dai yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

Mun samu cewa masu kamfanonin suna nuna tsoro ne ko kuma kin amincewa da karbar tallar dan takarar saboda gudun bi-baya daga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari ko kuma gwamnatin tarayya.

Tallar turmi: Kamfanonin talla suna bijirewa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar

Tallar turmi: Kamfanonin talla suna bijirewa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar
Source: UGC

KU KARANTA: Buhari ya zargi Kwankwaso da tafka sata

Legit.ng Hausa ta samu cewa duk da dai har yanzu hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC bata bayar da izinin fara kamfe ba, amma akalla ya zuwa yanzu kamfanonin talla 12 ne daga garin Abuja da Legas suka ki ansar tallar dan takarar.

A wani labarin kuma, Hukumar dake tallafawa 'yan gudun hijira ta gwamnatin kasat Norway watau Norwegian Refugee Council, (NRC) a turance ta bayyana cewa annobar cutar amai da zawo ta kashe akalla mutane 175 a jahohin Borno, Adamawa da Yobe tare da kwantar da kusan mutane dubu 10 a asibiti.

Haka zalika hukumar ta alakanta bulla tare da yaduwar cutar da yawa tare da cunkoson da ke a akwai a sansanonin 'yan gudun hijirar da aka ware wa wadanda ibtila'in rikicin ta'addancin Boko Haram ya rutsa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel