Gumi ya fadi hukuncin da ya dace a rika yiwa masu fyade

Gumi ya fadi hukuncin da ya dace a rika yiwa masu fyade

Babban malamin addinin musulunci da ke zaune a jihar Kaduna, Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin fyade ya cancanci hukuncin kisa kamar yadda ake yiwa masu fashi da makami.

Babban malaman ya fadi hakan ne a ranar Talata a garin Kaduna yayin da ya ke hira da Daily Trust a kan karuwar samun laifukan fyade a sassan kasan nan musamman a jihar ta Kaduna.

Ya bayyana cewar babu takamamen hukuncin fyade a karkashin shari'ar musulunci saboda babu damar yin fyade a garin da ake amfani da shari'ar musulunci na ainihi.

Gumi ya fadi hukuncin da ya dace a rika yiwa masu fyade

Gumi ya fadi hukuncin da ya dace a rika yiwa masu fyade
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kungiyar CAN ta tsoma baki cikin rikicin El-Rufai da Obi

Ya ce bayan karni na 6 na musulunci ne aka fara samun matsalar fyade bayan maza sun fara cudanya da mata.

"Akwai malaman da suka bayar da Fatwa cewa duk wani da ya yi amfani da makami ko barazanar zai kashe mutum wajen yin fyde ya cancanci hukuncin wanda ya yi dai-dai da na dan fashi da makami.

"Hakan ya nuna cewa duk wani wanda ya kwaikwayi dan fashi da makami saboda ya yi fyade ya cancanci hukuncin kisa," a cewar Gumi.

Shaihin malamin ya kara da cewa wanzuwar bayanai ta kafar intanet yana daga cikin hanyoyin da yara suke amfani dashi wajen kalon fina-finan batsa wadda hakan ma yana bayar da gudunmawa wajen wanzuwar fyade.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel