Gyran taku: Gwamnan APC ya gama shirin fita daga jam'iyyar, ya fara tura mukarraban sa

Gyran taku: Gwamnan APC ya gama shirin fita daga jam'iyyar, ya fara tura mukarraban sa

Da alamu dai rikicin cikin jam'iyyar dake mulki a Najeriya, ta All Progressives Congress (APC) zai dauki wani sabon salo biyo bayan labaran da muke samu na kammala shirye-shiren ficewa daga jam'iyyar da gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun yayi.

Binciken da majiyar mu ta jaridar Punch tayi dai ya bayyana cewa gwamnan yana sunsunar jam'iyyar adawa ta Democratic Peoples Party (DPP) ne kuma tuni har ma wasu makusantan sa da abokan siyasar sa sun soma shiga jam'iyyar.

Gyran taku: Gwamnan APC ya gama shirin fita daga jam'iyyar, ya fara tura mukarraban sa

Gyran taku: Gwamnan APC ya gama shirin fita daga jam'iyyar, ya fara tura mukarraban sa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: A'isha Buhari ta sa labule da 'yan Kannywood

Legit.ng Hausa dai ta samu cewa wannan dai ya biyo bayan rashin adalcin da gwamnan yace jam'iyyar ta sa tayi masa tare da magoya bayan sa a lokacin zabukan fitar da gwanin da ta shirya a jihar.

A wani labarin kuma, Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra kuma mataimakin dan takarar shugaban kasar Najeriya a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a ranar Asabar ne yayi wa Gwamnan jihar Kaduna wankin babban bargo tare da kashedi kan kalaman sa.

Tsohon gwamnan dai ya yi hakan ne a matsayin martani ga kalaman gwamnan na Kaduna, Nasiru El-rufa'i da ya kira shi mai tsattsauran ra'ayin kabilanci a ranar Juma'ar da ta gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel