Fada ya kacame: Ba sauran wani mai tunani da ya rage a jam'iyyar PDP - El-rufai

Fada ya kacame: Ba sauran wani mai tunani da ya rage a jam'iyyar PDP - El-rufai

Gwamnan jihar Kaduna kuma daya daga cikin jiga-jigan jam'iyya mai mulki ta APC, Malam Nasir El-rufai yayi wa jam'iyyar PDP kaca-kaca inda ya ce ba sauran mai tunani da ya rage a jam'iyyar yanzu.

Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a yayin da yake maida martani ga jam'iyyar ta PDP da a farko ta caccake shi biyo bayan kalaman gwamnan inda ya aibata tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi dake zaman mataimaki ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019.

Fada ya kacame: Ba sauran wani mai tunani da ya rage a jam'iyyar PDP - El-rufai

Fada ya kacame: Ba sauran wani mai tunani da ya rage a jam'iyyar PDP - El-rufai
Source: UGC

KU KARANTA: Wata kotu ta daure kasurgumin dan luwadi a Arewa

Legit.ng Hausa ta samu cewa a jiyan kalaman na gwamnan akan Mista Peter Obi da yace shi mai tsananin kabilanci ne, ya jawo cece-kuce da zafafan kalamai daga al'ummar Najeriya din wanda hakan ne ma ya sa jam'iyyar ta PDP ta fitar da sanarwa dauke da martani zuwa ga gwamnan.

A wani abarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Gombe dake a Arewa maso gabashin Najeriya sun samu nasarar cafke wani malamin Islamiyya mai suna Raudatul Qur’an mai shekaru 26 a duniya da laifin yiwa dalibar sa mai shekaru 5 fyade a ofishin sa.

Jami'an 'yan sandan yayin da suke nunawa manema labarai malamin mai suna Bilyaminu Halilu, tare da sauran masu laifin da suka kama sun bayyana cewa sun cafke shi ne a ranar 1 ga watan Oktoban da ya gabata a garin Gona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel