Tserewar Kanu: Kotun tarayya ta amince da gurfanar da tsohon minista da sanatan PDP

Tserewar Kanu: Kotun tarayya ta amince da gurfanar da tsohon minista da sanatan PDP

- Kotu Tarayya ta bayar da izinin gurfanar da wadanda suka karbi belin shugaban kungiayar IPOB, Nnamdi Kanu

- Wadanda suka karbi belin Kanu sun hada da Sanata Eyinnaya Abaribe, Tochukwu Uchendu da Emmanuel Shallom Ben

- Wannan ya biyo bayan gano cewar Kanu yana kasar Isra'ila ne inda daga baya ya bayyana cewar 'yan uwansa ne suka taimaka masa ya tsere

- Kafin wannan lokacin mutane da dama suna zargin gwamnatin tarayya da sace Kanu da kashe shi ciki har da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode

Babban kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar tilastawa hukumar yan sandan farin kaya DSS ta gurfanar da wadanda suka karbi belin shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a kotu bisa zarginsu da taimaka masa tserewa daga kasar kuma suka jaya baya suna tursasa soji ta fito dashi

Tserewar Kanu: Kotun tarayya ta amince da gurfnar da tsohon minista da sanatan PDP

Tserewar Kanu: Kotun tarayya ta amince da gurfnar da tsohon minista da sanatan PDP
Source: Twitter

Wani lauya mai suna Isiah Ayugu ne ya shigar da karar a gaban kotu inda alkalin kotun, Justice John Tsoho ya amince da karar ya kuma saka ranar 22 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a fara sauraran shari'an.

DUBA WANNAN: Hotunan irin tarbar da aka yiwa Buhari yayin da ya isa Paris

A karar, Ayugu yana bukatar a kama tsohon Ministan Sufurin Jiragen sama, Femi Fani Kayode da wadanda suka karbi belin Kanu a watan Afrilun 2017 wato Sanata Eyinnaya Abaribe, Tochukwu Uchendu da Emmanuel Shallom Ben.

Sauran wadanda mai shigar da karar ya ke bukatar a gurfanar a gaban kotu sun hada da Lauyan Kanu, ifeanyi Ejiofor, sai 'yan uwan shugaban na IPOB, Emmanuel Kanu da Uchechi Kanu wadanda suka rika yada jita-jitar cewa Sojin Najeriya sun sace Kanu sun kashe shi alhalin sun san cewa yana raye saboda sune suka taimaka masa ya fice daga kasar.

Lauyan ya shigar da wannan karar ne bayan wani faifan bidiyo ya fito a kwana-kwanan nan da ke nuna shugaban na IPOB, Nnamdi Kanu a kasar Isra'ila yana ibada kuma daga bisani aka yi hira da shi a wata kafar yada labarai na Isra'ilan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel