Hawainiyarka ta kiyayi ramar Peter Obi - PDP ta ja kunnen El-Rufai

Hawainiyarka ta kiyayi ramar Peter Obi - PDP ta ja kunnen El-Rufai

- Jam'iyyar adawa ta PDP ta gargadi Gwamna Nasir El-Rufai da ya kasance mai tauna magana kafin ya furta, ma damar akan Peter Obi ne

- PDP ta zargi El-Rufai, wanda ke shugabantar jihar Kaduna, da furta munanan kalaman da suka dade suna ciwa 'yan Nigeria tuwo a kwarya

- Jam'iyyar ta kuma bukaci gwamnan da ya fara tattara ya-nashi-ya-nashi don barin kujerarsa a 2019 kasancer zai sha kasa a babban zaben shekarar

A ranar Asabar, 10 ga watan Nuwamba, babbar jam'iyyar hamayya ta Nigeria, Peoples Democratic Party (PDP), ta gargadi Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, kan wasu kalamai daya furta ta take kallonsu kamar 'kalaman batanci' ga Peter Obi, abokin takarar Atiku Abubakar.

PDP ta zargi El-Rufai da cewar, ya kira Peter Obi, dan takarar mataimakin shugaban kasa karkashin jam'iyyar a zaben 2019, a matsayin mutum mai nuna kabilanci. Jam'iyyar ta bayyana Obi a matsayin dan kasa wanda bai kamata a alakantashi da nuna kabilanci ba.

Jam'iyyar PDP dai ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Kola Ologbondiyan, mai magana da yawun jam'iyyar, wacce aka rabawa manema labarai a Abuja.

KARANTA WANNAN: Karar kwana: Tawagar wani dan takarar gwamnan APC ta murkushe mata 2 har lahira a Rivers

Hawainiyarka ta kiyayi ramar Peter Obi - PDP ta ja kunnen El-Rufai

Hawainiyarka ta kiyayi ramar Peter Obi - PDP ta ja kunnen El-Rufai
Source: Facebook

Sanarwar wacce Legit.ng ta samu, ta bukaci El-Rufai da ya kasance mai tuna cewa zaben 2019 ba wai zai kasance na 'yar kiran sunaye ba, cin mutunci a yakin zabe ko kuma bata sunan dan takara, "Sai dai zai kasance hanya matabbaciya ta baiwa 'yan Nigeria damar sake baiwa PDP mulkin kasar."

"Don haka PDP tana shawartar Gwamna El-Rufai da ya fuskanci matsalolin da ke fuskantar jihar Kano wanda har ya sa jama'a suka yanke shawarar tsigeshi daga mulki a zaben 2019, tare da kaucewa shigar da kasar cikin rudanin siyasa ta hanyar furta kalaman da ka kiya kawo rabuwar kawuna saboda addini ko kabilanci.

"Ya zama ala-tilas El-Rufai ya guji furta irin kalaman da ka iya haddasa zubar da jini a jiharsa dama kasar baki daya.

"Daga kalaman El-Rufai, yanzu 'yan Nigeria sun gano wadanda ke daukar nauyin batancin da ake yiwa dan takarar shugaban kasarmu, Atiku Abubakar, da kuma abokin takararsa, Peter Obi."

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa Malam Nasir El-Rufai ya zargi Peter Obi da zama mutum mai nuna kabilanci.

El-Rufai, ya yi wannan zargin ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter a lokacin da yake tsoma baki kan rubutun da wata kungiya ta hadakalar masoyan Buhari-Osinbajo suka wallafa, inda ya dauko daga wani rubutu da jaridar Leadership ta wallafa na zargin Obi da korar 'yan Arewa daga jihar Anambra a lokacin da yake gwamnan jihar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel