Rundunar sojin sama sun kakkabe yan Boko Haram a sabon sansaninsu

Rundunar sojin sama sun kakkabe yan Boko Haram a sabon sansaninsu

- Jami'an sojin sama na Operation Lafiya Dole sun kakkabe yan ta’addan Boko Haram da yawa a aikin da suka gudanar

- Daraktan hulda da jama’a na NAF wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Asabar, 10 ga watan Nuwamba a Abuja, yace an gudanar da aikin ne a ranar Juma’a

- Kakkaban ya biyo bayan bayanan kwararru cewa yan Boko Haram sun dawo da wasu mayakansu daga tafkin Chadi da ke Arewacin Borno don sake kafa sabon sansani

Rundunar sojin sama ta ce jami’anta na Operation Lafiya Dole sun kakkabe yan ta’addan Boko Haram da yawa a aikin da suka gudanar a Talala a jihar Borno.

Air Commodore Ibikunle Daramola, daraktan hulda da jama’a na NAF wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Asabar, 10 ga watan Nuwamba a Abuja, yace an gudanar da aikin ne a ranar Juma’a, 9 ga watan Nuwamba.

Rundunar sojin sama sun kakkabe yan Boko Haram a Talala, Borno

Rundunar sojin sama sun kakkabe yan Boko Haram a Talala, Borno
Source: Twitter

Daramola ya ce aikin ya biyo bayan bayanan kwararru cewa yan Boko Haram sun dawo da wasu mayakansu daga tafkin Chadi da ke Arewacin Borno don sake kafa sabon sansani a hanyar yankin Talala-Aigin-Buk da ke jihar.

Kakakin rundunar yace aiki da rundunar sama zai taimaka matuka domin halaka sauran yan ta’addan a Borno.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta bayar da belin dan sandan da ya harbe ‘yar uwar tsohuwar ministan kudi

Shugaban Sojin Najeriya, Tukur Buratai, a ranar juma'a ya tabbatarwa da yan Najeriya nasara gurin yaki da kungiyar ta'addancin Boko Haram.

Tun a shekarar 2012,kungiyar ta kai farmaki masu yawa a sassan kasar,inda take kashe rayuka tare da Sace mutane.

Kungiyar ta'addancin ta yi sanadin rayuka 20,000 tare da kawo sanadin rasa muhallin sama da miliyan 2.4.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa na musamman, shafin NAIJ.com ya koma Legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel