An kama malamin makarantar islamiyya da yiwa dalibar sa fyade

An kama malamin makarantar islamiyya da yiwa dalibar sa fyade

Wani malamin makarantar Islamiyya, Bilyaminu Halilu, mai shekaru 26 ya shiga hannun jami'an 'yan sanda bayan samun sa da laifin yiwa dalibar sa mai shekaru 5 kacal a duniya fyade.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Gombe, Mohammed Mukaddas, ne ya gabatar da mai lafin ga taron manema labarai a ranar 1 ga watan Disamba.

Kwamishinan ya bayyana cewar Halilu na koyarwa ne a wata makarantar islamiyya mai suna "Raudatul Quranic Primary and secondary school' da ke by-pass a garin Gombe.

An kama malamin makarantar islamiyya da yiwa dalibar sa fyade

An kama malamin makarantar islamiyya da yiwa dalibar sa fyade
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan irin tarbar da aka yiwa Buhari yayin da ya isa Paris

Malamin ya kai yarinyar mai shekaru biyar biyar ofishinsa tare da yi mata fyade a kan tebur.

Asirin malamin ya tonu ne bayan mahaifiyar yarinyar ta ga jini a al'aurar ta yayin da ta zo yi mata wanka kuma da ta tambayeta, sai ta sanar da ita cewar malaminta ya ji mata ciwon a ofishinsa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa malamin ya amsa laifinsa a hannun jami'an tsaro, kamar yadda kwamishinan 'yan sandan ya sanar.

Kazalika ya bayyana cewar zasu gurfanar da shi a kotu ba tare da wani bata lokaci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel