Yadda wasu gwamnonin APC 6 suka shirya makarkashiyar da yasa DSS ta kama Oshiomhole

Yadda wasu gwamnonin APC 6 suka shirya makarkashiyar da yasa DSS ta kama Oshiomhole

- An gano cewar wasu gwamnonin APC guda 6 da ke fushi da Oshiomhole ne suka kai kararsa ga DSS

- Gwamnonin sunyi niyyar razana shugaban jam'iyyar ya yi murabus ne saboda su maye gurbinsa da wani da zai barsu su ci karensu ba babbaka

- Sai dai Oshiomhole ya doge kan cewar bai aikata kowanne laifi ba hakan ya sa bai sanya hannu kan takardan murabus din ba

- An kuma gano cewar akwai hannun wasu tsaffin 'yan APC da suka koma PDP a cikin makarkashiyar tsige Oshiomhole

Yadda jami'an DSS su ka tsare Oshiomhole na tsawon lokaci fiye da sa'a 8

Yadda jami'an DSS su ka tsare Oshiomhole na tsawon lokaci fiye da sa'a 8
Source: Depositphotos

A ranar Lahadi da ta gabata ne jami'an Hukumar Yan Sandan Farin Kaya (DSS) suka tsare shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole na tsawon sa'o'i 8 a ofishinsu inda su ka nemi ya yi murabus daga kujerarsa bisa tuhumarsa da karbar rashawa.

An gano cewa wasu gwamnonin jam'iyyar APC guda shida da ke fushi da Oshiomhole ne suka shigar da kararsa ga DSS din amma bai amince ya yi murabus din ba inda ya doge cewa bai aikata wani laifi ba.

Gwamnonin sun fito da daga yankunan Kudu maso Yamma, Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Gabas da Arewa maso Yamma.

DUBA WANNAN: Sarki Sanusi ya fadi jihar da ta fi jan hankalin masu saka hannun jari

Gwamnonin suna fushi ne saboda Oshiomhole bai bari sun nada wadanda suke son su gaje su ba a matsayin yan takarar gwamna a jihohinsu.

Akwai kishin-kishin din cewa wasu tsaffin 'ya'yan jam'iyyar APC da suka koma PDP sun bayar da gudunmawa wajen shirye-shirye tsige shugaban na APC saboda su gurgunta jam'iyyar musamman a yanzu da ake fuskantar zaben 2019.

Majiyar Legit.ng Hausa ta gano cewar wadanda suka shirya makarkashiyar sun san cewa shugaban na APC yana da niyyar fita kasar waje domin wata bukatarsa hakan ya sa su kayi kokarin dakile tafiyarsa.

Niyyar gwamnonin shine idan sunyi nasara kwatsam sai su mika wa shugaba Muhammadu Buhari takardan murabus din Oshiomhole ta yadda ba zai iya daukan wani matakin hana afkuwar hakan ba tun farko.

Wata majiya kwakwara ta tabbatar da cewar wasu daga cikin gwamnonin da suka shirya kamen sun tare a Abuja tun kafin DSS su gayyaci Oshiomhole har wani daga cikinsu ya shaidawa daya daga cikin 'yan kwamitin zabe cewar akwai 'wani babban abinda da zai faru a ranar Lahadi'.

A halin yanzu dai, shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin bincike kan lamarin domin warware matsalolin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel