An cafke wani da ke damfarar mutane da sunan Atiku a Facebook

An cafke wani da ke damfarar mutane da sunan Atiku a Facebook

Jami'an yan sanda masu binciken sirri (IRT) sunyi nasarar damke wani Aminu Ahmed Yerima wanda ya yaudari mutane sama da 50 a Facebook da sunan cewa shi hadimin dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ne.

Vanguard ta ruwaito cewar Yerima ya fito ne daga karamar hukumar Jada ne a jihar Adamawa wato karamar hukumar daya da tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar.

Asirinsa ya tonu ne bayan wasu mata biyu Raliat da Awa Maje cikin wadanda ya damfara sun shigar da kara ofishin yan sanda inda su kace ya karbe musu kudi har N5 miliyan cikin watanni shida.

An cafke wani da ke damfarar mutane da sunan Atiku a Facebook

An cafke wani da ke damfarar mutane da sunan Atiku a Facebook
Source: Facebook

Majiyar yan sanda ta bayyana cewa IGP na yan sanda ya bayar da umurnin rundunar IRT da ke karkashin jagorancin Abba Kyari tayi bincike ta gano gaskiya lamarin. An gano Yarima ne ta hanyar amfani da bayanan da ya bayar a shafinsa na Facebook.

DUBA WANNAN: Ya kashe matar sa da yayansa bayan ya kama su turmi da tabarya

Yan sandan sun ce Yarima ya bude shafin Facebook ne inda ya yi amfani da hotunansa da ya dauke tare da Atiku a wurare da yawa ciki har da wanda suka dauka a Saudiyya kuma ya rika fadawa mutane cewa yana yiwa Atiku aiki.

Yarima ya rika fadawa mutane cewa Atiku ya kan bayar da taimakon kudade ga mutane kuma zai taimaka musu domin su samu kudin kuma mutane da dama sun yarda cewa zai iya musu hanya su samu kudi daga hannun Atiku.

"Atiku mutum ne mai saukin kai kuma duk lokacin da ya zo gari ya kan bari mutane su shiga gidansa su gana da shi har ma su dauki hotuna tare. Na dauki hotuna da shi a gidansa da kuma a Saudiyya da muka hadu lokacin aikin hajji.

"Ina fadawa mutane cewa zan iya taimaka musu su samu taimakon kudi daga Atiku amma ina tambaya su bani kudin mota da zanyi tafiya in same shi saboda shi mutum ne mai tafiye-tafiye, da zarar sun bani sai in dena amsa su a Facebook daga baya ma in dakile shafinsu," inji Yarima.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel