Makomar Oshiomhole a APC: Buhari, Osibanjo, Tinubu, gwamnoni za su gana mako mai zuwa

Makomar Oshiomhole a APC: Buhari, Osibanjo, Tinubu, gwamnoni za su gana mako mai zuwa

- Shuwagabannin jam'iyya mai mulki ta APC za su gudanar da taro a mako mai zuwa, don yanke hukunci kan makomar Adams Oshiomhole, wanda idon kowa ya koma kansa

- Wani jigo a cikin jam'iyyar, ya bayyana cewa gabanin zuwan ranar taron, tuni uban jam'iyyar na kasa, Asiwaju Ahmed Tinubu, da kuma Oshiomhole, suka gana a birnin Farisa

- Rahotanni sun nuna cewa wasu gwamnonin jam'iyyar da suka harzuka, sun fara tuntubar mambobin kwamitin gudanarwa, don tilasta Oshiomhole sauka daga mukaminsa

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu daga jaridar PUNCH, na nuni da cewa, za a gudanar da wani taro na shuwagabannin jam'iyya mai mulki ta APC a mako mai zuwa, inda a nan ne za a yanke hukunci kan makomar shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, wanda idon kowa ya koma kansa.

Wani jigo a cikin jam'iyyar, wanda ya zanta da jaridar a Abuja a ranar Juma'a, ya kuma bukaci a sakaya sunansa saboda karfin lamarin, ya bayyana cewa gabanin zuwan ranar taron, tuni uban jam'iyyar na kasa, Asiwaju Ahmed Tinubu, da kuma Oshiomhole, suka gana a birnin Farisa, kasar Faransa a ranar Alhamis.

Ya kara da cewa ganawar tsakanin Tinubu da Oshiomhole ta mafi mayar da hankali ne kan yadda wasu mambobin jam'iyyar suka harzuka tare da tayar da jijiyon wuya akan lallai sai an tunbuke Oshiomhole daga shugabancin kasar, cikin mambobin kuwa, gwamnoni ne suka fi karfafa wannan bukatar.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: INEC ta cika alkawarinta na haramtawa APC gabatar da 'yan takara a jihar Zamfara

Makomar Oshiomhole a APC: Buhari, Osibanjo, Tinubu, gwamnoni za su gana mako mai zuwa

Makomar Oshiomhole a APC: Buhari, Osibanjo, Tinubu, gwamnoni za su gana mako mai zuwa
Source: Facebook

Tsohon gwamnan jihar ta Legas, na daya daga cikin jigogin jam'iyyar da ke goyon bayan Oshiomhole, wanda a yanzu yake fuskantar tuhuma daga hukumar tsaron cikin gida ta fararen kaya DSS.

Wata majiya daga jam'iyyar APC ta ce, "Tinubu da Oshiomhole sun hadu a birnin Farisa a ranar Alhamis, kan yadda wasu gwamnoni da mambobin kwamirin gudanarwar jam'iyyar ke kokarin tsige shugaban jam'iyyar daga kujerarsa. Idan za a iya tunawa, Asiwaju ne ya samawa Oshiomhole hanya har ya zama shugaban jam'iyyar, lokacin da Chief Oyegun ya bukaci karin wa'adin shugabanci.

"Yanzu da lamarin har ya kai hukumar tsaro ta DSS ta fara tuhumar Oshiomhole, kuma an hura masa wuta akan ya sauka, dole ne ta sa ya tsere don haduwa da Tinubu, don ya san shi kadai ne zai iya cetonsa. Har yanzu, bamu san dabarar da zasu yi amfani da ita wajen hana wannan tuhuma ba."

Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin gwamnonin jam'iyyar da suka harzuka, sun fara tuntubar wasu daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa, don tilasta Oshiomhole sauka daga mukaminsa, har sai hukumar DSS ta kammala binciken tuhumar da ta ke masa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel