Tsuntun da ya ja ruwa: Wani Gwamnan APC ya fadi rawar da ya taka wajen jefa Oshiomhole cikin tsomomuwa

Tsuntun da ya ja ruwa: Wani Gwamnan APC ya fadi rawar da ya taka wajen jefa Oshiomhole cikin tsomomuwa

Gwamnan Jihar Ogun dake a kudu maso yammacin Najeriya, Ibikunle Amosun, ya ce babu hannun sa a cikin gayyatar da jami’an SSS suka yinwa Shugaban Jam’iyyar APC Kwamared Adams Oshiomhole da suka shafe awoyi suna yimasa tambayoyi.

A baya dai an ruwaito cewa Oshiomhole ya sha tambayoyi ne a ranar Lahadin da ta gabata, dangane da wasu zarge-zargen da wasu gwamnanonin APC suka rubuta cewa shugaban na APC ya kakkarbi kudaden toshiyar baki a lokacin da ake ta hada-hadar gudanar da zabukan fidda gwani na ‘yan takarar APC a fadin kasar nan.

Tsuntun da ya ja ruwa: Wani Gwamnan APC ya fadi rawar da ya taka wajen jefa Oshiomhole cikin tsomomuwa

Tsuntun da ya ja ruwa: Wani Gwamnan APC ya fadi rawar da ya taka wajen jefa Oshiomhole cikin tsomomuwa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: INEC ta wallafa sunayen 'yan takarar gwamna

Legit.ng Hausa ta samu cewa Gwamna Amosun na daya daga cikin masu rikici da Oshiomhole, tun bayan da dan takarar da ya ke so ya gaje shi, Adekunle Akinlade ya sha kaye a hannun Dapo Abiodun. Sauran gwamnonin da ke rikici da Oshimhole sun hada da Rochas Okorocha na Imo da Abdulziz Yari na Zamfara.

A wani labarin kuma, Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) shiyyar jihar Legas ta bayyana cewa tuni shirye-shirye suka yi nisa tsakanin ta da gwamnan jihar ta Legas Akinwumi Ambode da sauran 'yan jam'iyyar da dama don gani ta zawarto su zuwa jam'iyyar daga All Progressives Congress (APC).

Jam'iyyar ta PDP ta ce tana iya bakin kokarin ta wajen ganin ta fahimtar da dukkan wadanda aka batawa rai a APC din sun dawo a jam'iyyar su tare kuma da basu tabbacin kyakkyawan adalci a sabuwar jam'iyyar ta su idan suka amince.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel