An kama wani malamin islamiyya da laifin yiwa dalibar sa mai shekara 5 fyade a Arewa

An kama wani malamin islamiyya da laifin yiwa dalibar sa mai shekara 5 fyade a Arewa

Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Gombe dake a Arewa maso gabashin Najeriya sun samu nasarar cafke wani malamin Islamiyya mai suna Raudatul Qur’an mai shekaru 26 a duniya da laifin yiwa dalibar sa mai shekaru 5 fyade a ofishin sa.

Jami'an 'yan sandan yayin da suke nunawa manema labarai malamin mai suna Bilyaminu Halilu, tare da sauran masu laifin da suka kama sun bayyana cewa sun cafke shi ne a ranar 1 ga watan Oktoban da ya gabata a garin Gona.

An kama wani malamin islamiyya da laifin yiwa dalibar sa mai shekara 5 fyade a Arewa

An kama wani malamin islamiyya da laifin yiwa dalibar sa mai shekara 5 fyade a Arewa
Source: Facebook

KU KARANTA: Cikin sirri, Buhari ya nada surikin sa a babban mukami

Legit.ng Hausa ta samu cewa yadda asirin malamin ya tonu shine da mahaifiyar yarinyar ta ga jini na fita daga al'aurar ta sadda take yi mata wanka inda yarinyar ta zayyana mata cewa malamin ne ya labbace ta ya kai ta ofishin sa ya kuma yi lalata da ita.

Tuni dai malamin ya amsa laifin sa kuma da zarar yan sandan sun kammala bincike sun ce za su kai shi kotu domin ya fuskanci hukuncin da ya dace da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel