Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun budewa motar sojoji wuta, akalla mutane 9 sun hallaka

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun budewa motar sojoji wuta, akalla mutane 9 sun hallaka

Akalla mutane tara sun rasa rayukansu da yammacin jiya yayinda yan tada kayar bayan Boko Haram suka budewa motar sojoji wuta a babban titin Maiduguri/Ngala ranan Alhamis, jaridar Sahara Reporters ta bada rahoto.

Wannan hari ya faru ne a Musena da Logmani misalin karfe shida na yamma.

Yan Boko Haram sun budewa motar sojojin wuta tare da kashe fasinjoji takwas da soja daya. Sauran fasinjojin sun arce cikin daji.

"Majiyar ya bayyana cewa: “Mun kai ziyara wajen ranan Juma’a. Mutane tara sun rasa rayukansu; mutanen nan basu da tausayi, sun yiwa wani direba ruwan harsasai kuma suka kona sauran,”

“Akalla motoci biyar masu dauke da kayayyakin masarufi sun bace kuma yan ta’addan sun kona wasu motoci shida, har da babban mota.”

Wannan abu na faruwa ne kimanin sa’o’I 24 bayan wadannan yan ta’adda suka kai hari kauyen Kareto, kimanin kilomit 20 daga birnin Damaturu a jihar Yobe.

KU KARANTA: Hukumar Kwastam ta damke kwantena cike kayan Sojoji da makamai a jihar Ribas

A wani labarin kuma wasu mayakan Boko Haram sun kai mugun samame a yankin kudancin jahar Borno a daren Talata, inda suka yi sacen sacen kayayyakin abinci, daga bisani suka banka ma duk wani gida dake kauyen wuta, suka tsere.

Legit.com ta ruwaito cewar a sakamakon wannan harin mazauna kauyen na Kala dake kusa da karamar hukumar Damboa sun yi batan dabo, ko sama ko kasa an nemesu an rasa har bayan tafiyan yan ta’addan.

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar ma majiyarmu cewa da misalin karfe 9 na daren Talata yan ta’addan suka kunno kai cikin kauyen, inda suka bude ma mazauna kauyen wuta irin na mai kan uwa da wabi, wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu, wasu kuma suka jikkata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel