Da dumin sa: Hukumar INEC ta wallafa sunayen wadanda za suyi takarar Gwamna a zaben 2019

Da dumin sa: Hukumar INEC ta wallafa sunayen wadanda za suyi takarar Gwamna a zaben 2019

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) ta soma sakin sunayen wadanda za suyi takarar kujerun gwamnoni a jahohin Najeriya ashirin da hudu da za'a gudanar da zabukan shekarar 2019.

Haka zalika mun samu cewa hukumar zaben har ila yau ta soma fitar da sunayen wadanda za suyi takarar kujerun 'yan majalisun jahohin tarayyar Najeriya dukkan su da za'a gudanar da zabukan su a shekarar ta 2019.

Da dumin sa: Hukumar INEC ta wallafa sunayen wadanda za suyi takarar Gwamna a zaben 2019

Da dumin sa: Hukumar INEC ta wallafa sunayen wadanda za suyi takarar Gwamna a zaben 2019
Source: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon yadda ake wanke dakin Ka'abah

Legit.ng Hausa ta samu cewa kafin hukumar ta wallafa sunayen, ana ta samun rikice-rikice a jahohi da dama musamman game da 'yan takarkarin gwamnoni na jam'iyyar APC mai mulki wanda har ma ake tunanin rikicin ka iya kara rincabewa.

A wani labarin kuma, Ministan yada abarai na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari Alhaji Lai Mohammed a ranar Laraba ya ce rahoton da kwamitin duba zuwa ga yiwuwar karin alabashin ma'aikata da suka mika wa shugaba Buhari na Naira dubu 30, shawara ce kawai ba wani abu ba.

Ministan yace har yanzu shugaban kasar bai yanke hukunci ba game da matsayar sa akan batun har sai ya yi duba na tsanaki ga rahoton tukuna sannan ya fitar da matsayar sa wadda ake sa ran ta zama ta karshe akan batun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel