PDP na kulla wani makirci don lashe zaben 2019 – Kungiya

PDP na kulla wani makirci don lashe zaben 2019 – Kungiya

- Wata kungiyar jama’a karkashin inuwar Nigeria Network (SNN) ta zargi jam’iyyar PDP da kulla wani makirci don lashe zaben 2019 ta kowani hali

- Kungiya ta ce sun gama shirya yin amfani da karya a kamfen din 2019 ta hanyar amfani da manyan hukumomin gwamnati

- Sun ce PDP ta kammala shiri tsaf domin cimma manufarta ta hanyar kamfen na yaudara

Wata gamayyar kungiyar jama’a karkashin inuwar Nigeria Network (SNN) ta bayyana cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kulla wani makirci don lashe zaben 2019 ta kowani hali.

Sakataren kungiyar, Patience Daniel yayinda yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, 9 ga watan Nuwamba yace an gama shirya yin amfani da karya a kamfen din 2019 ta hanyar amfani da manyan hukumomin gwamnati.

PDP na kulla wani makirci don lashe zaben 2019 – Kungiya

PDP na kulla wani makirci don lashe zaben 2019 – Kungiya
Source: Twitter

Kungiyar ta yi zargin cewa babbar jam’iyyar adawa ta kammala shiri tsaf domin cimma manufarta ta hanyar kamfen na yaudara.

KU KARANTA KUMA: Majalisa za ta soke N-Power idan ya koma siyasa - Shehu Sani

A wani lamari na daban mun ji cewa majalisar wakilai ta tarayya ta yanke hukunci kafa wani kwamiti na musamman da zai yi kwakkwaran bincike kan irin yadda jam'iyyun siyasa suka yiwa dokokin zabe karan tsaye a lokacin da suka gudanar da zabukan fitar da gwani. '

A jiya Alhamis, majalisar ta ce kwamitin zai kuma yi kwakkwaran bincike kan kudaden shigar manyan jam'iyyun siyasar kasar, tun daga shekaru hudu da suka gabata, kamar yadda sashe na 226 na kundin mulkin kasar na 1999 (kamar yadda aka sake fasalinsa) ya hassalewa majalisar yin hakan.

Da wannan, yan majalisun suka tafka muhawara, kan "Dakile majalisun wakilan tarayya daga zama kamar karnukan farauta hannun gwamnoni ko da a nan gaba."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel