Sarki Sanusi ya fadi jihar da ta fi jan hankalin masu saka hannun jari

Sarki Sanusi ya fadi jihar da ta fi jan hankalin masu saka hannun jari

Sarkin Kano, Mai Martaba Muhammadu Sanusu II (CON) kuma ciyaman din Qua Iboe Power Project (QIPP) ya yi amanna cewar jihar Akwa Ibom itace tafi dacewa da duk wani mai neman saka jari a Najeriya.

Sarkin ya yi wannan jawabin ne a wata ziyara da ya kai wa Gwamna Udom Emmanuel a gidan gwamnatin jihar da ke Uyo inda ya jinjina wa gwamnan kan nasarorin da ya samu a jihar tun hawarsa kujerar gwamna.

Sarki Sanusi ya bayyana cewa ya dade yana bibiyar irin ayyukan cigaba da gwamnan ke gudanarwa a jihar a fanonin samar da ababen more rayuwa, zaman lafiya da samar da tsaro a jihar.

Sarki Sanusi ya fadi jihar mafi dacewa da saka jari a Najeriya

Sarki Sanusi ya fadi jihar mafi dacewa da saka jari a Najeriya
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnan Najeriya ya karaya, ya ce Allah ne kadai zai iya da Najeriya

Sarkin ya kuma bayyana cewa kamfaninsa na QIPP za ta saka hannun jari na $1.1 biliyan a harkar hakar iskar gas a jihar ta Akwa Ibom.

"Bayan saka hannun jarin, za a gina masana'antar sarrafa iskar gas wadda za ta rika samar da mega watts na lantarki 540 da al'ummar Najeriya za su amfana dashi," inji Sanusi.

A cewar Sarki Sanusi, an zabi jihar Akwa Ibom ne domin saka hannun jarin saboda tana da dukkan abinda ake bukata wato iskar gas, zaman lafiya da kuma al'umma da su iya aiki a kamfanin.

A jawabinsa, Gwamna Emmanuel ya yabawa Sarkin bisa ziyarar da ya kawo masa da kuma zuwa jiharsa domin saka hannun jari. Ya kara da cewa yana sanar da dukkan al'ummar duniya cewa Akwa Ibom tana maraba da masu saka hannun jari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel