Da duminsa: Rikici ya barke a majalisar dokokin jihar Ondo, yan majalisa sun raunata

Da duminsa: Rikici ya barke a majalisar dokokin jihar Ondo, yan majalisa sun raunata

Yan baranda sun kai farmaki majalisar dokokin jihar Ondo jim kadan bayan tsige kakakin majalisar, Hanarabul Bamidele David Oloyelogun.

An tsige Bamidele David Oloyelogun, a yau Juma’a tare da mataimakin kakakin, Ugundeji Iroji, bisa ga zargin rashin kwarewa, babakere na saba doka.

Yan barandan da ake kyautata zaton mambobin kungiyar yan tasha ne karkashin shugabansu Jacob Dabo suka kai farmaki majalisar dokokin.

Sun shiga majalisar da makamai masu hadari irinsu gorori, duwatsu, kwalabe, inda suka jikkata yan majalisu hudu duk da kasancewan jami’an tsaro.

KU KARANTA: Jihohi goma dake samun matsalar network yayin yin waya, katsewar layi - NCC

Hazakalika sun lalata dukiyar miliyoyin naira irinsu motoci. Wannan abu bai bar yan jarida a baya ba inda aka fitittikesu daga zauren majalisan da kwaleben giya.

Mun kawo muku rahoton cewa Majalisar jihar Ondo ta tsige Kakakin majalisar, Rt. (Hon) Bamidele David Oloyelogun a zamanta na safiyar yau Juma'a kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

An tsige Oloyelogun ne tare da mataimakinsa Hon. Ogundeji Iroju duk a zaman majalisar na jiya.

Yan majalisar 18 cikin 26 ne suka rattaba hannu kan kuri'ar amincewa da tsige shugabanin majalisar bisa dalilan almubuzzaranci da kudi, girman kai da babakere da kuma amfani da matsayinsu wajen karya dokoki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel