Ya san yana da kanjamau amma yayi wa yara kusan 70 fyade

Ya san yana da kanjamau amma yayi wa yara kusan 70 fyade

- An kama wani soja da yake dauke da cutar HIV

- Yana lalata da kananun yara

- Yanayi musu barazanar watsa hotunan su

Ya san yana da kanjamau amma yayi wa yara kusan 70 fyade

Ya san yana da kanjamau amma yayi wa yara kusan 70 fyade
Source: UGC

Jami'an yan sandan kasar Thailand sun samu nasarar cafke wani soja wanda yake dauke da cuta mai karya garkuwar jiki HIV.

Sojan mai suna Maj.Jakkrit Khomsing yana dauke da cutar HIV sannan yayi lalata da yara sama da 70 masu shekaru 13-18.

Khomsing yana fara cewa su turo masa hoton su Wanda suke tsirara ta hanyar kafar sadarwa.

Idan ya nuna musu bukatar shi sukaki amincewa sai yayi musu barazanar watsa hotunan su wadanda suke tsirara.

DUBA WANNAN: NCC: Yadda kamfanonin sadarwa ke kwarar jama'a

Yan sandan sun samu maganin HIV a lokacin da sukaje kama Khomsing a gidan shi a ranar Laraba.

Daga nan ne akaje akayi masa gwajin jini inda sakamako ya nuna cewa yana dauke da cutar ta HIV.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel