An zabi mata 19 a matsayin alkalai a Amurka

An zabi mata 19 a matsayin alkalai a Amurka

- Kasar Amurka ta zabi mata 19 a matsayin alkalai a birnin Houston na jihar Texas

- Hakan ya faranta ran mutanen yankin musamman ma a shafukan zumunta

- Wannan shine karona farko da hakan ke faruwa a tarihi

Labari da ke zuwa mana sun nuna cewa kasar Amurka ta kafa tarihi a ranar Talata, 6 ga watan Nuwamba bayan da aka zabi mata 19 a matsayin alkalai a birnin Houston na jihar Texas, shafin BBC Hausa ya ruwaito.

Wannan babban matsayi da matan suka samu ya haddasa farin ciki a jihar musamman ma a kafofin sada zumunta.

An zabi mata 19 a matsayin alkalai a Amurka

An zabi mata 19 a matsayin alkalai a Amurka
Source: UGC

Wani hoton matan, wanda ake kira Houston 19, wanda aka dauka a watan Agusta ya yi ice da shahara a shafin sada zumunta na Twitter.

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da jami'in rundunar 'yan sanda da ake zargin ya kashe Miss Anita Akapson

Yankin Harris na da adadin mutane miliyan hudu da rabi, kuma shi ne mafi girma a jihar Texas, kuma na uku mafi girma a Amurka.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa na a hanyarsa na dawowa Najeriya daga kasar Amurka.

Shugaban APC ya fita wajen kasar bayan jami’an hukumar yan sandan farin kaya sun bincike shi akan zargin kaban cin hanci a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel