Yanzu Yanzu: Oshiomhole na a hanyar dawowa Najeriya

Yanzu Yanzu: Oshiomhole na a hanyar dawowa Najeriya

Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa na a hanyarsa na dawowa Najeriya daga kasar Amurka.

Shugaban APC ya fita wajen kasar bayan jami’an hukumar yan sandan farin kaya sun bincike shi akan zargin kaban cin hanci a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Da fari, Legit.ng ta rahoto cewa tsohongwamnan najihar Edo ya shiga hannun DSS bayan korafin cewa ya karbi cin hanci daga hannun was yan takara a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Yanzu Yanzu: Oshiomhole na a hanyar dawowa Najeriya

Yanzu Yanzu: Oshiomhole na a hanyar dawowa Najeriya
Source: Depositphotos

Sai dai sabbin bayanai da ke billowa ya nuna cewa zuwan Oshiomhole Amurka bai da nasaba da siyasa domin ance matarsa, Iara na kasar Amurka tana jinya.

KU KARANTA KUMA: Majalisa za ta soke N-Power idan ya koma siyasa - Shehu Sani

An tattaro cewa ya baro Ladan zuwa Lagas a jirgin Birtaniya a safiyar ranar Juma’a, 9 ga watan Nuwamba.

Tsohon shugaban na kungiyar kwadago na Najeriya (NLC), zai sake fuskantar rikicin zaben fidda gwani da ya tafi ya bari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel