Majalisa za ta soke N-Power idan ya koma siyasa - Shehu Sani

Majalisa za ta soke N-Power idan ya koma siyasa - Shehu Sani

Majalisar dattawa ta bayyana cewa za ta aiwatar da bincike akan zargin siyasantar da shirin N-Power da ake ganin wasu yan siysa na yi don zaben 2019.

Majalisar ta kafa wani kwamiti saboda su bincikei lamarin cewa shirin da ke bayar da tallafin kudi ga talakawa yanzu ya koma wata hanyar da 'yan siyasa ke raba wa magoya bayansu a yayin da zabe ke gabatowa.

Sanata Shehu Sani wanda ya sauya sheka daga jam'iyya mai mulki zuwa PRP ya bayana cewa idan har suka gano shirin na N-Power ya koma na siyasa za su bukaci a tsayar da shi.

Sai dai kuma gwamnatin tarayya ta karyata zargin, inda Barista Ismail Ahmad, babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan shirin tallafa wa al'umma, ya bayana hakan a matsayin makirci na kushewa da cin zarafin shirin.

Ya ce babu ruwan shirin da wata jam'iyya, domin kasuwa a ke shiga a zakulo masu kananan sana'o'i domin ba su tallafi ba tare nuna wariya ba.

KU KARANA KUMA: Yanzu Yanzu: Sunan dan takarar gwamna na APC a Imo ya bace bat yayinda INEC ta saki sunaye 67

Ya kuma ce a shirye suke su je su kare kansu idan har kwamitin bincike da majalisar dattawa ta kafa ya gayyace su domin gurfana a gabansa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel