Majalisar wakilai za ta binciki badakalar da jam'iyyu suka yi a zabukan fitar da gwani

Majalisar wakilai za ta binciki badakalar da jam'iyyu suka yi a zabukan fitar da gwani

- Majalisar wakilai ta tarayya ta yanke hukunci kafa wani kwamiti na musamman da zai yi bincike kan yadda jam'iyyun siyasa suka gudanar da zabukan fitar da gwani

- Kwamitin zai kuma yi kwakkwaran bincike kan kudaden shigar manyan jam'iyyun siyasar kasar, tun daga shekaru hudu da suka gabata

- Da wannan, yan majalisun suka tafka muhawara, kan "Dakile majalisun wakilan tarayya daga zama kamar karnukan farauta hannun gwamnoni ko da a nan gaba."

Majalisar wakilai ta tarayya ta yanke hukunci kafa wani kwamiti na musamman da zai yi kwakkwaran bincike kan irin yadda jam'iyyun siyasa suka yiwa dokokin zabe karan tsaye a lokacin da suka gudanar da zabukan fitar da gwani.

A jiya Alhamis, majalisar ta ce kwamitin zai kuma yi kwakkwaran bincike kan kudaden shigar manyan jam'iyyun siyasar kasar, tun daga shekaru hudu da suka gabata, kamar yadda sashe na 226 na kundin mulkin kasar na 1999 (kamar yadda aka sake fasalinsa) ya hassalewa majalisar yin hakan.

Da wannan, yan majalisun suka tafka muhawara, kan "Dakile majalisun wakilan tarayya daga zama kamar karnukan farauta hannun gwamnoni ko da a nan gaba."

KARANTA WANNAN: An gurfanar da magidanci bisa gazawarsa na gabatar da matarsa da ta damfari banki N180m

Majalisar wakilai za ta binciki badakalar da jam'iyyu suka yi a zabukan fitar da gwani

Majalisar wakilai za ta binciki badakalar da jam'iyyu suka yi a zabukan fitar da gwani
Source: Depositphotos

Wannan hukunci da majalisar ta yanke, ya biyo bayan wani kudirin doka da Chika Adamu (APC, Niger) ya gabatar kan "Gurguntar da demokaradiyyar cikin gida da wasu jam'iyyun siyasa suka yi a lokacin gudanar da zaben fitar da gwani don fuskantar babban zaben 2019."

Adamu, wanda ya jagoranci muhawarar, ya bayyana damuwarsa kan yadda rahotanni ke yawo na irin aka tafka kuskure a zabukan fitar da gwani da jam'iyyu suka gudanar, inda ya zargi cewa da yawa daga cikin jam'iyyun sun yi fatali da dokokin zaben kasar.

"Wasu daga cikin jam'iyyun sun ki gudanar da zabuka a wasu jihohi wanda ya ci karo da sashe na 87 sakin layi na (10) na kudin dokokin zabe, da ya tilastawa kowacce jam'iyyar gudanar da zabukan fitar da gwani.

KARANTA WANNAN: Saura kiris APC ta gama tarwatsewa - Hasashen Dino Melaye

"Idan har majalisa ba ta dauki mataki akan wannan mummuna aika aikar da wasu jam'iyyu suka gudanar a zabukan fitar da gwani ba, to kuwa ina jin tsoron cewa majalisar na iya komawa kamar karen farautar gwamnoni, da kuma lalata demokaradiyyar da zaben kasa a nan gaba," cewar Adamu.

Ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda wasu jam'iyyu suka musanya sunayen yan takarar da suka lashe zaben fitar da gwanin da sunayen wasu yan takarar daban, wanda hakan ya tauye hakkin masu kada kuri'a, tare da cin karo da sahe na 87 na kundin dokokin zaben kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel