Yanzu Yanzu: Sunan dan takarar gwamna na APC a Imo ya bace bat yayinda INEC ta saki sunaye 67

Yanzu Yanzu: Sunan dan takarar gwamna na APC a Imo ya bace bat yayinda INEC ta saki sunaye 67

- Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta saki sunayen yan takarar gwamna 67 na zaben 2019

- Sai da sunan dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Imo ya bace bat a cikin jerin sunayen da hukumar ta saki

- Ana ganin rashin ganin sunan nasa baya rasa nasaba da umurnin kotu na cewa kada a buga kowani suna a APC tunda har yanzu Magana na kotu

Sunan dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Imo ya bace bat a cikin jerin sunayen da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta saki a ranar Juma’a, 9 ga watan Nuwamba.

Yayinda sunan dan takarar Peoples Democratic Party (PDP), Emeka Ihedioha da wasu 66 ya shiga jerin, ba’a ga na dan takarar APC ba.

Idan za ku tuna an samu sabani tsakanin Cif Uche Nwosu wanda ya kasance surukin gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha da Sanata Hope Uzodinma kan wanda ya cancanci zama dan takarar APC.

Yayinda Okorocha yace lallai surukinsa ne ya lashe zaben fidda gwani na gwamna a jihar shugaban jam’yyar na kasa, Adams Oshiomhole ya nuna Sanata Uzodinma a matsayin dan takara. Hakan ya sa aka garzaya kotu.

KU KARANTA KUMA: El-Zakzaky: Yan Shi’a sun karyata Lai Mohammed kan cewa ana ciyar da shugabansu N3.5m duk wata

Sai dai ana ganin rashin ganin sunan nasa baya rasa nasaba da umurnin kotu na cewa kada a buga kowani suna a APC tunda har yanzu Magana na kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel