Yanzu yanzu: Buhari ya shilla kasar Faransa a nahiyar Turai

Yanzu yanzu: Buhari ya shilla kasar Faransa a nahiyar Turai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shilla kasar Faransa a ranar juma’a don halartar wani muhimmin taro da za’yi akan zaman lafiya a birnin Paris a ranar Lahadi, 11 ga watan Nuwamba zuwa ranar Talata 13 ga watan Nuwamba.

Legit.com ta ruwaito kaakakin shugaban kasa Femi Adesina ne ya sanar da haka cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a daga fadar shugaban kasa, inda yace gwamnatin kasar Faransa ce ta shirya wannan taro tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi masu zaman kansu.

KU KARANTA: Manyan shuwagabannin kungiyar Izala sun jaddada goyon bayansu ga Ganduje

A cewar Adesina “An gina taron ne akan cewa lallai sai da hadin kan kasashen Duniya za’a samar da dawwamammen zaman lafiya a sassan Duniya gaba daya da sauran kalubalen dake addabar kasashen Duniya.

Yanzu yanzu: Buhari ya shilla kasar Faransa a nahiyar Turai
Buhari
Asali: Facebook

Kaakakin shugaban kasa Adesina ya bayyana cewa shugaba Buhari zai bi sawun jerin shuwagabannin duniya da shugaban majalisar dinkin Duniya Antonio Gutteres inda zasu tattauna akan matsalolin da suka ki ci suka ki cinyewa a duniya gaba daya.

Haka zalika a yayin taron, shuwagabannin kasashen Duniya zasu taron tunawa da yarjejeniyar sulhu da aka yi a ranar 11 ga watan Nuwambar 1918 tsakanin dakarun kasashen Duniya da kasar Jamus a dajin Compiegne dake kasar Faransa bayan yakin Duniya na daya, wanda ya cika shekaru 100.

Bugu da kari shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron zai karbi bakoncin shugaba Buhari a wata liyafar cin abinci da zai shirya kafin a kai ga fara taron, bayan an kammala taron kuma Buhari zai gana da yan Najeriya mazauna kasar Faransa.

Daga cikin wadanda zasu take ma Buhari baya zuwa wannan taro akwai gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari, gwamnan Anambra, Willie Obiano da sabon gwamnan jahar Ekiti Kayode Fayemi.

Sauran yan rakiyan sun hada da ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama, Ministan shari’a Abubakar Malami, mashawarcin Buhari akan harkokin tsaro Babagana Munguno, sai kuma shugaban hukumar leken asiri Ahmad Rufai Abubakar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel