Saura kiris APC ta gama tarwatsewa - Hasashen Dino Melaye

Saura kiris APC ta gama tarwatsewa - Hasashen Dino Melaye

- Sanata Dino Melaye ya yi hasashen cewa tsohuwar jam'iyyarsa ta APC za ta tarwatse nan ba da jimawa ba

- Melaye, dan majalisar dattijai mai wakiltar mazabar Kogi ta Yamma, bai bayyana dalilinsa na wannan hasashe na tsarwatsewar APC ba

- Sanatan dai kawai ya ce dukkanin alkawarin da ta dauka ta soke su, hakan ne ma ya sa ya yiwa jam'iyyar shagube duk da a cikinta ne ya lashe zaben 2015

A ranar Juma'a 09 ga watan Nuwamba, Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta Yamma, a majalisar dattijai ta kasa, Dino Melaye, ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC mai mulki na daf da tarwatsewa.

Sai dai, Dino Melaye bai wani bada wasu kwararan hujjoji ko dogon bayani kan dalilinsa na wannan hasashe ba, kawai daiya ce babu abunda zai hana jam'iyyar ta APC ta tarwatse.

"Tarwatsewar APC wani lamari ne da ya zama wajibi. Duk wasu alkawura an soke su har sai mun sake haduwa," kamar yadda Melaye ya wallafa a shafinsa na Twitter.

KARANTA WANNAN: Hukumar Kwastam ta cafke mutane hudu tare da kama motocin alfarma da kayyakin N240m

Saura kiris APC ta gama tarwatsewa - Hasashen Dino Melaye

Saura kiris APC ta gama tarwatsewa - Hasashen Dino Melaye
Source: Depositphotos

Melaye dai ya samu nasarar zama sanata ne karkashin jam'iyyar APC a zaben 2015, sai dai ya sauya sheka zuwa jam'iyyar hamayya ta PDP, tare da wasu takwarorinsa na majalisar.

Yana daya daga cikin manyan jiga jigan da ke nuna tsantsar adawarsu ga wannan gwamnati mai ci a yanzu karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Haka zalika, sanatan ya kasance daya daga ciki yan siyasar da suka dade suna takun saka da gwamnan jihar sa, Yahaya Bello. A baya bayan nan, Melaye ya zargi Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da kulla makircin kashe shi da kuma hanashi yakin zabe a mazabarsa.

Melaye ya yi ikirarin cewa, ya rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa, majalisar dinkin duniya, ofishin jakadancin kasar Burtaniya, CJN, AU, ECOWAS, Jamus da Kanada, don sanar da su wannan yunkuri da ake yi na kawar da shi daga doron kasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel