Ku mutunta doka – Hukumar Birtaniya ga yan Shi’a da hukumomin tsaro

Ku mutunta doka – Hukumar Birtaniya ga yan Shi’a da hukumomin tsaro

Biyo bayan kazamar karo da aka yi tsakanin hukumomin tsaron kasar da kungiyar yan Shi’a, babban kwamishinan Birtaniya a Najeriya mai shirin barin gado, Paul Arkwright ya bukaci bangarorin biyu da su mutunta doka.

Aridar Punch ta ruwaito cewa Arkwright wanda ya bayyana hakan a Abuja a ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba yayinda yake zantawa da manema labarai akan karon da aka yi tsakanin yan Shi’a da sooi wanda yayi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane ya kuma yaba ma gwamnatin tarayya kan kokarin ta na tabbatar da cewar an magance lamarin.

Ku mutunta doka – Hukumar Birtaniya ga yan Shi’a da hukumomin tsaro

Ku mutunta doka – Hukumar Birtaniya ga yan Shi’a da hukumomin tsaro
Source: Depositphotos

Ya kuma kara da cewa koda dai yan Shi’a na da yancin yin zanga-zangar lumana, ya zama dole hukumomin tsaro su yi taka tsan-tsan domin gujema kisan bayin Allah da basu ji basu gani ba.

Legit.ng ta tattaro cewa jakadan ya kuma daura hakkin rikici da ke tsakanin makiyaya da manoma akan sauyin yanayi sabanin yadda mutane ke alakanta rikicin da na addini.

KU KARANTA KUMA: Amurka, Faransa sun nuna sha'awarsu kan Nigeria Air - Gwamnatin tarayya

A baya mun ji cewa Sanata Abdullahi Gumel ya bayyana cewa rashin ingantaccen ci gaba da kuma kayayyakin more rayuwa a garuruwan iyakar kasar na daga cikin manyan dalilan da suka sanya rikici da rashin tsaro kamar yadda yayi korafi cewa idan dare ya yi za ku ga wutar lantarki a garuruwan iyakar Kamaru amma babu wuta a na Najeriya.

Gumel, shugaban kwamitin maalisar dattawa kan jihohi da kananan hukumomi ya bayyana hakan a wani hira da manema labarai bayan ziyarar gani da ido da suka kai don ganin ci gaban iyakar kaqsar a Abuja.

Dan majalisan ya daura kalubalen akan rashin isashen kudi ga hukumomin iyakar kasar, inda hakan kan haddasa rashin tsaro da ci gaban rikici a garuruwa sama da 90 a fadin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel