Idan dare ya yi za ku ga iyakar garuruwan Kamaru da wuta amma babu wuta a na Najeriya – Sanata Gumel

Idan dare ya yi za ku ga iyakar garuruwan Kamaru da wuta amma babu wuta a na Najeriya – Sanata Gumel

Sanata Abdullahi Gumel ya bayyana cewa rashin ingantaccen ci gaba da kuma kayayyakin more rayuwa a garuruwan iyakar kasar na daga cikin manyan dalilan da suka sanya rikici da rashin tsaro kamar yadda yayi korafi cewa idan dare ya yi za ku ga wutar lantarki a garuruwan iyakar Kamaru amma babu wuta a na Najeriya.

Gumel, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan jihohi da kananan hukumomi ya bayyana hakan a wani hira da manema labarai bayan ziyarar gani da ido da suka kai don ganin ci gaban iyakar kasar a Abuja.

Dan majalisan ya daura kalubalen akan rashin isashen kudi ga hukumomin iyakar kasar, inda hakan kan haddasa rashin tsaro da ci gaban rikici a garuruwa sama da 90 a fadin kasar.

Idan dare ya yi za ku ga iyakar garuruwan Kamaru da wuta amma babu wuta a na Najeriya – Sanata Gumel

Idan dare ya yi za ku ga iyakar garuruwan Kamaru da wuta amma babu wuta a na Najeriya – Sanata Gumel
Source: UGC

Yace rashin isashen kudi ga hukumomin, wanda shine zai kawo karshen matsalolin da inganta garuruwan iyakar abun damuwa ne.

KU KARANTA KUMA: An dage shari’ar Gwamnati da Ekweremadu sai shekara mai zuwa

Gumel ya ce akwai bukatar daukar mataki domin kawo karshen matsalolin da garuruwan iyakar kasar ke fuskanta ta fannin tsaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel