Saraki ya ba wadanda ambaliya yayi wa barna a Jihar Kwara kyautar Miliyan 10

Saraki ya ba wadanda ambaliya yayi wa barna a Jihar Kwara kyautar Miliyan 10

Mun samu labari cewa wasu Bayin Allah da su ka gamu da ambaliya a Jihar Kwara kwanaki sun ga abin alheri daga hannun Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki inda ya ba su kyautar makudan kudi.

Saraki ya ba wadanda ambaliya yayi wa barna a Jihar Kwara kyautar Miliyan 10

Wadanda ambaliya ya aukawa sun ga abin alheri daga wajen Bukola Saraki
Source: Depositphotos

Abubakar Bukola Saraki ya raba kyautan kudi har Naira Miliyan 10 ga wasu mutane kusan 630 da ambaliya yayi wa barna kwanaki a Yankin tsakiyar Kwara. Saraki ya raba wannan kyauta ne a ofishin sa da ke mazabar sa a cikin Garin Ilorin.

Alhaji Musa Abdullahi wanda shi ne Darekta Janar na ofishin Mazabar Saraki na ABS da ke Garin Ilorin shi ne ya raba wannan kudi a madadin Shugaban Majalisar. An yi wani gajeren biki kafin a raba wadannan makudan kudi a Jihar ta Kwara.

Musa Abdullahi yace wannan kadan ne daga cikin taimakon da Saraki ya saba jama’an sa ba tare da la’akari da banbanci na siyasa ba. Sai dai Darektan na ofishin ABS ya nemi wadanda aka yi wannan agaji su zabi Jam’iyyar PDP a 2019.

KU KARANTA: Rigimar APC: Gwamnonin Jihohi su na neman a tsige Oshimhole

Darektan ofishin ‘Dan Majalisar yace Dr Abubakar Bukola Saraki ya damu da halin da jama’an sa su ke ciki don haka ya ba su wannan agaji a dalilin ibtila’in da ya same su. A lokacin da abin ya faru dai Dr. Saraki ya raba kayan agajin gaggawa.

Alhaji Yusuf Jimoh da kuma Alhaja Adijat Baki wadanda aka rabawa wannan kudi sun bayyanawa ‘Yan jaridar Daily Trust cewa sun ji dadin wannan abin kirki da aka yi masu inda su kace za su dage kwarai wajen ganin PDP ta ci zaben 2019.

Kusan dai Bukola Saraki ne kadai ‘Dan siyasar da ya kawowa mutanen agaji a lokacin da su ka gamu da wannan musiba. Kwanaki kuma Sanatan ya raba makudan kudi ga’Yan kasuwan da ke cikin Jihar Kwara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel