Zargin rashawa: Buhari ne ya hana DSS bincikar Oshiomhole - PDP

Zargin rashawa: Buhari ne ya hana DSS bincikar Oshiomhole - PDP

Har yanzu dai jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba ta ce uffan ba kan zargin karbar rashawa da ake yiwa shugabanta, Adams Oshiomhole wanda hakan ya janyo hukumar DSS ta gayacce shi a jiya domin amsa tambayoyi.

A jiya, mai magana da yawun jam'iyyar, Lanre Issa-Onilu ya bayyana cewar ba shi da wata masaniyya kan abinda ya faru tsakanin Oshiomhole da jami'an hukumar DSS a karshen makon da ya gabata a Abuja.

"Bamu da wani bayyani kan wannan jita-jitam. Hasali ma, Ciyaman din na mu ya fita kasar waje balle ya tabbatar da ya karyata wannan jita-jitan. Duk lokacin da muka samu karin bayani zamu sanar da al'umma," inji shi.

Zargin rashawa: Buhari ne ya hanna DSS bincikar Oshiomhole - PDP

Zargin rashawa: Buhari ne ya hanna DSS bincikar Oshiomhole - PDP
Source: UGC

DUBA WANNAN: Gwamnan Najeriya ya karaya, ya ce Allah ne kadai zai iya da Najeriya

Issa-Onilu ya mayar da martani ne kan rahoton da wani kafar yadda labarai na intanet ya wallafa inda ya bayyana cewa jami'an DSS sun gayyaci Oshiomhole sunyi masa tambayoyi har na tsawon sa'o'i 9 sakamakon zarginsa da karbar rashawa yayin zaben cikin gida da wasu gwamnonin APC su kayi.

Majiyar tayi ikirarin cewar DSS sun shawarci Oshiomhole ya yi murabus amma bai amince ba inda ya ce musu babu abinda zai sa ya yi murabus muddin shugaba Muhammadu Buhari yana goyon bayansa.

Oshiomhole ya samu matsala da gwamnonin jihar Zamfara da Ogun da Imo saboda ba su samu ikon bawa dan takarar da suke so tikitin zaben gwamna ba.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi ikirarin cewar shugaba Muhammadu Buhari yana kokarin yin rufa-rufa kan zargin cin hanci da rashawar da ake zargin Oshiomhole da hannu ciki.

A sakon da ta fitar a jiya, PDP tayi ikirarin cewar shugaba Muhammadu Buhari ne ya tilastawa hukumar DSS sakin Oshiomhole duk da cewa akwai zargin rashawa da cin hanci da ake masa.

Jam'iyyar ta ce shugaba Buhari ba shi da hurumin yin magana kan yaki da rashawa muddin bai bari hukumar DSS ta gudanar da binciken ta ba tare da yi mata katsalandan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel